Dukiyar Dangote Ta Ragu da Dala Miliyan 400, Ya Sauka Zuwa Lamba Na 2 a Jerin Attajiran Forbes Africa
- A cikin sa'o'i 24, Dangote ya yi asarar dala miliyan 400, wanda ya sa ya nesanci matsayin Johann Rupert a jerin attajirai
- Raguwar darajar dukiyar Dangote dai ta faru ne bisa nasaba da faduwar darajar Naira idan aka kwantanta da dala
- Duk da haka, Dangote ya ci gaba da zama na daya a jerin attajiran Bloomberg, inda aka ce yana da kudin da ya kai dala biliyan 17
Aliko Dangote dai ya sake samun koma baya a yawan kudinsa sakamakon faduwar darajar Naira, lamarin da ya rage darajar kadarorinsa da dukiyarsa na koma kasa da dala biliyan 11.
Arzikin attajirin na Najeriya ya ragu daga dala biliyan 11.2 a ranar 4 ga watan Agusta zuwa dala biliyan 10.8, ya samu faduwar dala miliyan 400 kenan a rana daya kacal a cewar Forbes.
A halin yanzu, a cikin jerin attajirai da aka sabunta a ranar 5 ga Agusta, 2023, Dangote ya koma matsayinsa na daya, inda dukiyarsa ta haura dala biliyan 13.5 ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Ya aka yi darajar kudinsa ta ragu?
Wannan dai ya biyo bayan rahoton da Legit.ng ta samu a baya cewa attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya ya sauka a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka, mukamin da ya kwashe sama da shekaru goma a kai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A baya dai dukiyar Dangote ta karu zuwa dala biliyan 11.2, wanda hakan ya sa ya samu damar kwato kambun attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka.
Duk da haka, raguwar dukiyarsa a baya-bayan nan ta mayar da shi bayan Johann Rupert, wanda a halin yanzu ke rike da kambun na Dangote a baya da dukiyarsa da ta kai dala biliyan 11.2.
Matsayin Dangote a Forbes da Bloomberg
Kasancewar galibin kadarorin Dangote na Naira ne, ana iya danganta raguwar darajar dukiyarsa da karyewar darajar Naira.
Da arzikin da ya kai dala biliyan 10.8, Forbes ta saka Aliko Dangote a matsayin mutum na biyu mafi arziki a nahiyar Afrika; a Bloomberg kuma yana kan matsayin na daya da adadin kudi sama da dala biliyan 17.
Kamfanoni 10 da Damgote ya mallaka
A bangare guda, Aliko Dangote, dan Najeriyan da ya fi kowa kudi a Afrika kuma mamallakin Dangote Group fitacce ne wajen gina kasuwanci da fafutukar hada-hada a fannoni da yawa.
Bloomberg ta ruwaito cewa, rukunin kamfanin Dangote na harkalla ne ta sukari, siminti da kuma wani fannin da ake kira Nascon Allied Industries.
Wadannan kamfanonin sun kafu da kafafunsu a matsayin na gaba-gaba wajen samar da siminti, sukari da kayayyakin abinci a Najeriya da ma bangarori da yawa a nahiyar Afrika.
Asali: Legit.ng