Yan Bindiga Sun Sace Mutane 7 Tare Da Halaka Manomi a Jihar Kaduna

Yan Bindiga Sun Sace Mutane 7 Tare Da Halaka Manomi a Jihar Kaduna

  • Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun halaka manomi tare da sace mutane bakwai
  • Lamarin ya faru ne a Unguwar Gajere da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna
  • Mazauna yankin sun koka kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga da kan janyo asarar rayuka da dukiyoyi

Kaduna - Yan ta'adda da ake zaton masu garkuwa da mutane ne, sun halaka mutum ɗaya tare sace wasu mutane bakwai a Unguwar Gajere da ke mazaɓar Kutemeshi da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna.

An bayyana cewa lamarin dai ya faru ne ranar Laraba, 2 ga watan Agustan shekarar 2023, inda maharan suka farmaki mutanen yayin da suke aiki a gonakinsu.

Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
Yan bindiga sun halaka manomi tare da sace mutane bakwai a jihar Kaduna. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Ayyukan 'yan ta'adda sun munana a yankin

Dan Majalisar jihar da ke wakiltar mazaɓar Kakanga ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce 'yan bindigan sun kuma yi awon gaba da dabbobi masu tarin yawa a wasu ƙauyuka da ke makwabtaka da su.

Kara karanta wannan

Tinubu: Adadin Ministocin Da Shugabannin Najeriya Suka Naɗa Daga 1999 Zuwa Yau

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce ƙauyukan Gwandu da Damari ne ɓarayin ke yawan zuwa domin satar shanu da sauran dabbobi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma ce yankin ya yi matuƙar ɓaci da ayyukan 'yan ta'adda, waɗanda sai dai fatan Ubangiji ya yi maganinsu.

Mazauna ƙauyukan sun saba da hare-haren

Wani daga cikin mazauna ƙauyukan da ke fama da ayyukan 'yan ta'addan mai suna Isa Haruna, ya bayyana cewa kusan kullum sai an kawo hari a yankin na su.

Ya ƙara da cewa yanzu haka mutanen yankin sun fara sabawa da hare-haren da 'yan bindigar ke kai wa.

Ya yi kira ga hukumomin da suka da ce da su kawo musu ɗauki kan wannan ƙangi da suka tsinci kawunansu a ciki kamar yadda ya zo a rahoton na Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kyakkyawan Kurma Ya Koka Kan Rashin Samun Budurwa, Ya Ce 'Yan Mata Sun Ki Yarda Su Yi Soyayya Da Shi

Sojoji sun halaka riƙaƙƙun 'yan Ta'adda Ado Aliero da Dankarami

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan nasarar halaka riƙaƙƙun 'yan ta'adda da jami'an sojin Najeriya suka yi a wani sabon farmaki da suka kai.

Luguden wutar da rundunar sojin sama ta yi a jihar Zamfara, ya yi sanadin kashe 'yan ta'adda 10, ciki kuwa har da Ado Aliero da kuma Dankarami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

iiq_pixel