Kano: Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Mutane Fiye Da 60 Da Ke Aikata Muggan Laifuka Daban-daban

Kano: Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Mutane Fiye Da 60 Da Ke Aikata Muggan Laifuka Daban-daban

  • Jami'an 'yan sandan Kano sun kama akalla mutane da ake zargi da aikata manyan laifuka fiye da 60
  • Kakakin rundunar a jihar, SP Haruna Kiyawa shi ya bayyana haka a madadin kwamishinan 'yan sanda, Muhammad Gumel a yau Juma'a
  • Ya ce kwamishinan ya bada umarnin kamo sauran 'yan daba uku da suka ki mika wuya tare da alkawarin ba da kyautar kudi N100,000 ga ko wannensu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan Kano ta kama mutane fiye da 60 a cikin mako biyu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya bayyana haka a yau Juma'a 4 ga watan Agusta a Kano yayin gabatar da masu laifin.

'Yan sanda a Kano sun kama matasa fiye da 60 da ake zargi da aikata laifuka da dama
Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Cafke Da Dama Kan Zargin Laifuka Daban-daban. Hoto: PR News.
Source: Facebook

Ya ce wadanda aka kaman sun hada da 'yan daba da masu safarar kwayoyi sai kuma masu kwacen babura da motoci, Peoples Gazette ta tattaro.

Kara karanta wannan

'Yan Daba Sun Afka Wa Manyan APC, Sun Barnata Kayayyaki Na Miliyoyi, Bayanai Sun Fito

Yadda aka samu muggan makamai a hannun tsagerun

Kiyawa ya ce an samu muggan makamai da kwayoyi da kuma kayayyakin da aka sace wa jama'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

SP Kiyawa ya yi jawabi a madadin kwamishinan 'yan sandan Kano, Muhammad Gumel, PM News ta tattaro.

Ya ce sun bi umarnin babban Sifetan 'yan sanda ne, Kayode Egbetokun na kakkabe dukkan masu aikata laifuka.

Gumel ya ware N100,000 ga duk wanda ya kawo 'yan daba uku

Ya ce:

"A kan haka ne jami'an 'yan sanda suka kai farmaki dutsen Dala inda kashi 99 na 'yan daban suka tuba tare da mika makamansu.
'Yan daban har ila yau, sun yi alkawarin ci gaba da aiki tare da jami'an tsaro da kuma taimakonsu.
"Kan haka kwamishinan 'yan sandan Kano, Gumel ya ba da umarnin kai samame kan wadanda suka ki mika wuya inda ya ce zai ba da kyautar N100,000 ga kowa ne daya daga cikinsu."

Kara karanta wannan

Yan Sandan Kano Na Neman Wasu 'Yan Daba 3 Ruwa A Jallo, Za A Ba Da Kyautan Kudi Ga Wanda Ya Ba Da Bayani A Kansu

Yan Sanda Sun Ware Kyautar Kudi Ga Wanda Ya Ke Da Bayani Kan Wasu 'Yan Daba 3 A Kano

A wani labarin, 'yan sandan Kano sun ware N100,000 ga duk wanda ya kawo bayanan da za su kai ga kama wasu gawurtattun 'yan daba a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Muhammad Gumel shi ya bayyana haka inda ya ce sun karbi tubabbun 'yan daba da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.