Jerin Ministoci: Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Maye Gurbin Maryam Shetti Da Abokiyar Karatunta Mariya Mahmoud

Jerin Ministoci: Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Maye Gurbin Maryam Shetti Da Abokiyar Karatunta Mariya Mahmoud

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sunan Maryam Shetty majalisa domin tantanceta a matsayin minista
  • Kwatsam bayan Shetty ta isa majalisa don a tantanceta sai ta samu labarin maye gurbinta da abokiyar karatunta, Mariya Mahmoud
  • Mutane sun soki nada Shetty a mukamin minista domin dai ana yi mata kallon yar TikTok ce kuma ana ganin ba za ta taka rawar gani a mukamin minista ba

Abun da ba a taba zato ba ya faru a ranar Juma'a, 4 ga watan Agusta, lokacin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga jerin ministocinsa na biyu sannan ya maye gurbinta da sunan Mariya Mahmoud; abokiyar karatunta a baya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Ms Shetty ta sha suka game da halinta da kuma cewa ba za ta iya tafiyar da aikin minista ba.

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Maryam Shetty Da Tinubu Ya Sauya Sunanta A Jerin Ministoci

Tinubu ya maye gurbin Ms Shetty da Mariya Mahmoud
Jerin Ministoci: Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Maye Gurbin Maryam Shetti Da Yar Ajinsu Mariya Mahmoud Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Salau Buhari and Shams A Imam
Asali: Facebook

Mutane da dama na daukar Shetty a matsayin yar TikTok saboda tarin mabiya da take da su a fadin dandalin sada zumunta da dama.

Da isarta (Ms Shetty) majalisar dokokin tarayya don a tantanceta a matsayin minista, sai ta ga cewa an cire ta daga jerin wadanda aka mika sunansu majalisar dattawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An maye gurbin sunanta da na Ms Mahmoud, abokiyar karatunta a makarantar sakandare na Kano Foundation Secondary School da kuma jami'ar Bayero na Kano.

An kuma tattaro cewa matan biyu sun kasance abokan karatu a jami'a, inda suke daukar darasin likitanci a tare yayin da Shetty ke karantar bangaren motsa jiki, Mahmoud ta kasance dalibar likitanci da tiyata.

Mahmoud ta kasance daya daga cikin kwamishinonin da ke kusa da iyalin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Ta kuma kasance kawar Amina Ganduje, daya daga cikin shahararrun yaran shugaban jam'iyyar All Progressive Congress (APC) na yanzu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Maryam Shetty Ta Samu Labarin Cire Sunanta a Cikin Majalisa, Abinda Ta Yi Ya Ja Hankali

Amina Ganduje ma likitace wacce ta kammala karatunta daga jami'ar Maiduguri sannan ta yi aiki a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH).

Ana ta rade-radin cewa Amina ta zabi kwamishinoni biyu ko fiye da haka a majalisar mahaifinta, da Mahmoud a matsayin daya daga cikinsu.

Yadda Maryam Shetty ta samu labarin cire sunanta cikin ministoci

A gefe guda, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Maryam Shetty tana cikin zauren majalisar dattawa a lokacin da ta samu labarin cire sunanta daga jerin ministoci.

Maryam Shettima, wacce aka fi sani da suna Maryam Shetty, tana ɗaya daga cikin sunayen ministoci 19 da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya miƙa majalisa ranar Laraba, 2 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel