Tura Dakaru Nijar: Shehu Sani Ya Buƙaci Sanatoci Su Duba Girman Abinda Suke Shirin Yi
- Sanata Shehu Sani ya faɗawa Majalisar Dattawa abinda ya kamata ta yi dangane da buƙatar da Tinubu ya aiko ma ta
- Tinubu ya aike da wasiƙa zuwa majalisar, wacce ke shaida musu shirye-shiryen da yake na tura dakarun soji Nijar
- Sai dai Shehu Sani ya shawarci sanatocin da su duba girman abin da kuma sakamakon da ka iya biyowa baya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi kira ga Majalisar Dattawan Najeriya da ta duba girman buƙatar da Tinubu ya aiko ma ta da kuma abinda ka iya zuwa ya dawo.
Shehu na magana ne kan wasiƙar da Tinubu ya tura Majalisar Dattawa, yana mai shaida musu cewa yana shirin tura dakarun soji jamhuriyar Nijar.
Shehu a cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya shawarci Tinubu da kar ya bari ƙasashen turawa su zuga shi faɗawa yaƙi da jamhuriyar Nijar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shehu ya yi Allah wadai da katse wutar lantarkin Nijar da aka yi
Ya nemi sanatocin musamman ma waɗanda suka fito daga jihohin da suka yi iyaka da Nijar, da su duba abinda tura sojojin zai iya haifarwa.
Shehu Sani ya kuma yi Allah wadai da matakan dakatar da ba da wutar lantarki ga jamhuriyar ta Nijar da Najeriya ta yi.
Ya kuma shawarci Tinubu da ya ci gaba da bin matakai na diflomasiyya wajen shawo kan lamarin ba ƙoƙarin amfani da ƙarfin soji ba.
Atiku ya yi tsokaci game da juyin mulkin jamhuriyar Nijar
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton tsokacin da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi kan shirin daukar matakin soji kan Nijar.
Atiku ya ce matakai na diflomasiyya ya kamata ECOWAS ta ɗauka ba wai matakan amfani da ƙarfi ba.
Atiku ya ce yin amfani da ƙarfin soji zai iya rura wutar rikicin da ake fatan a ga ya lafa.
Hukumar shige da fice ta ƙasa ta gargadi 'yan Najeriya kan zuwa Nijar
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan gargaɗin da hukumar kula da shige da fice ta ƙasa ta yi wa 'yan Najeriya kan zuwa jamhuriyar Nijar.
Hukumar ta shawarci 'yan Najeriya da su yi zamansu a cikin gida Najeriya har zuwa lokacin da abubuwa za su lafa.
Asali: Legit.ng