Jarumin Fim Ɗin Najeriya Pete Edochie, Ya Ce Shan Barasa Ya Kusa Aika Shi Lahira
- Jarumin Nollywood Pete Edochie, ya bayyana yadda barasa ta kusa janyo masa tafiya barzahu
- Ya ce barasar da ya ƙyanƙyama ce ta sanya shi afkawa wata babbar mota da aka ajiye a gefen titi
- Edochie ya kuma yi magana kan mace-macen auren da ake yawan samu a masana'antar ta Nollywood
Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood Pete Edochie, ya bayyana yadda shan barasa ya kusa aika shi lahira.
Ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da ya yi da fitaccen mai watsa shirye-shiryen nan Chude Jideonwo da aka wallafa a shafinsa na Instagram.
Yadda lamarin ya faru, Edochie ya ba da labari
Pete Edochie ya bayyana cewa a ranar 14 ga watan Mayun shekarar 1977 ne ya kusa baƙuntar lahira, sakamakon tuƙa mota da ya yi alhalin yana cikin maye na barasar da ya sha.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce a ranar ya fito garin Nsukka ne a motarsa da zummar zuwa wani wuri, inda bacci ya kwashe shi a yayin da yake tuƙa motar.
Edochie ya ce a cikin hakan ne ya je ya afkawa wata babbar mota da ke tsaye a gefen titi, wanda daga nan ya sulmiya cikin daji.
Sai dai jarumin ya miƙa godiyarsa wurin Ubangiji bisa ceton rayuwarsa da ya yi.
Ya ce dole ne mata su riƙa haƙuri a rayuwar aure
Da yake tsokaci kan mace-macen auren da ake yawan samu a masana'antar, Edochie ya ce dole ne mata su sauya tunaninsu game da rayuwar aure.
Ya ce ma fi yawan jarumai mata 'yan masana'antar ta su da suka yi aure shekaru biyu zuwa uku nan baya, duk sun fito daga gidajen mazajen na su.
Ya shawarci mata da su sanya a ransu cewa dole ne su yi haƙuri kuma su yi biyayya domin samun rayuwar aure tabbatacciya.
Ya ce kuskuren da da yawa ke yi daga cikinsu shi ne tunanin cewa aure abu ne mai sauƙi, wanda kuma ba haka ba ne.
A yanzu haka ɗan jarumin mai suna Yul Edochie na fuskantar ƙara da matarsa ta shigar a gaban kotu, inda ta nemi a raba aurensu saboda ƙara wani auren da ya yi.
Jarumar fim ta goyi bayan Tinubu kan cire tallafin man fetur
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan jarumar finafinan Nollywood Eniola Badmus, da ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Tinubu kan cire tallafin man fetur.
Jarumar ta ce 'yan Najeriya da dama ba su da masaniya kan alfanun cire tallafin man fetur ɗin da shugaban ya yi.
Asali: Legit.ng