Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Shirinsa Na Tura Sojoji Nijar Ga Majalisar Dattawa

Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Shirinsa Na Tura Sojoji Nijar Ga Majalisar Dattawa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da majalisar tarayya shirin ƙungiyar ECOWAS na ɗaukar matakai kan jamhuriyar Nijar
  • A wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta, Tinubu ya jero matakan da zasu ɗauka
  • Wannan na zuwa ne bayan koƙarin tattaunawar neman maslaha da sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum ta ci tura

FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike da saƙo ga majalisar dattawa yana mai sanar da shirin ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) na ɗaukar matakai kan jamhuriyar Nijar.

Shugaban ya sanar da Majalisar dokokin kasar cewa ECOWAS na shirin daukar matakin soji da sauran takunkumi kan masu juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Shirinsa Na Tura Sojoji Nijar Ga Majalisar Dattawa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Daily Trust ta ce ya bayyana haka ne a wata wasiƙa da ya tura zuwa majalisar kuma shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ƙaranta a zaman yau Jumu'a.

Kara karanta wannan

Jamhuriyar Nijar Ta Ɗauka Mataki Mai Tsauri Kan Najeriya da Wasu Ƙasashe Bayan Sulhu Ya Rushe

A wasiƙar, an ji shugaba Tinubu na cewa bayan abubuwa marasa dadi da suka auku a Nijar, wanda ta kai ga hambarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ECOWAS ta yi tir da lamarin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙara da cewa ECOWAS karƙashin jagorancinsa ta cimma matsayar tabbatar da dawo da zaɓaɓɓiyar gwamnatin Demokuraɗiyya a Nijar a taron da ta gudanar, Daily Post ta rahoto

Jerin matakan da ECOWAS zata ɗauka kan gwamnatin mulkin soji a Nijar

Da yake jero matakan da ECOWAS ta amince zata ɗauka kan gwamnatin Sojin Nijar a wasiƙar da aike wa Sanatoci, shugaba Tinubu ya ce:

"ECOWAS ta amince da ɗaukar matakai da suka ƙunshi, rufewa da lura da dukkan iyakokin kasa da jamhuriyar Nijar da sake farfado da aikin hako kan iyakokin."
“Katse wutar lantarki ga Nijar. Tattara tallafin kasashen duniya don aiwatar da shirin ECOWAS. Hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da na musamman zuwa ciki ko fitowa Jamhuriyar Nijar."

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Tsokaci Game Da Juyin Mulkin Nijar, Ya Fadi Matakan Da Ya Kamata ECOWAS Ta Ɗauka

"Dakatar da shigar abinci Nijar daga Legas da tashar jiragen ruwa. Wayar da kan yan Najeriya kan muhimmancin waɗan nan matakn. Ɗaukar matakin soji kan masu juyin mulkin Nijar idan suka ƙi bada haɗin kai."

Tinubu Ya Janye Maryam Shetty, Ya Maye Gurbinta Da Mahmud Daga Kano

A wani labarin kuma Shugaba Bola Tinubu ya maye gurbin daya cikin mutanen da ya zaba don nada wa minista, Maryam Shetty, ya kuma zabi wasu sabbi biyu.

An sanar da hakan ne lokacin da Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya karanto wasikar shugaban kasar a zauren Majalisa a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262