Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Mafi Karanci Za a Nunka Wa Ma'aikata Albashi a Najeriya

Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Mafi Karanci Za a Nunka Wa Ma'aikata Albashi a Najeriya

  • Fadar shugaban ƙasa ta bayyana irin tanadin da Tinubu ke wa ma'aikata domin yaye musu wahalhalun cire tallafin fetur
  • Mai magana da yawun shugaba Bola Tinubu ya ce mafi karanci za a nunka albashin ma'aikata a sabon mafi karancin albashi
  • Ya ce tun a wurin taron NEC na baya-bayan nan gwamnatocin jihohi suka aminta zasu rungumi sabon mafi ƙarancin albashi

FCT Abuja - Mai bai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shawara ta musamman kan harkokin midiya da yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya yi magana kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Kakakin shugaban ƙasan ya ce ma'aikata su sa ran samun aƙalla ninkin albashin da suke ƙarba yanzu idan aka aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a Najeriya.

Kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale.
Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Mafi Karanci Za a Nunka Wa Ma'aikata Albashi a Najeriya
Asali: UGC

Mista Ngelale ya bayyana haka ne yayin da yake ƙarin haske kan matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka domin rage radaɗin cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

"Yan Najeriya Suna Farin Ciki da Mulkinka" An Faɗa Wa Shugaba Tinubu Halin da Mutane Ke Ciki

Hadimin shugaban ƙasar ya yi wannan furucin ne a cikin shirin Siyasa a Yau na kafar talabijin ɗin Channels.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

FG zata nunka wa ma'aikata albashi

Jaridar Daily Trust ta rahoto kakakin shugaban yana cewa:

"Ba na so in yi katsalandan a aikin shugaban kasa ko aikin kwamitin mafi karancin albashi da ke kokarin cimma matsaya."
"Amma abin da zan ce shi ne shugaban kasa ba zai aminta da komai ba face akalla rubanya albashin ma'aikata, ina nufin ninka mafi ƙarancin albashi na yanzu."
“Zuwa watan Yuni, 2023, jihohi 36 sun samu Naira biliyan 300 fiye da yadda suka samu a kowane wata da ya gabata cikin shekaru biyu da suka shige. Sun riga sun sami ƙarin kuɗi a yanzu."
“Gwamnatin tarayya a nata bangaren tana ƙoƙarin rage tsadar abinci da makamashi ta hanyar tallafa wa kamfanonin sufuri da kuma samar da ayyukan noma, da bada jari ga kananan yan kasuwa."

Kara karanta wannan

Tsadar Mai: IPMAN Ta Koka, Ta Bayyana Yadda 'Yan Kasuwar Man Fetur Ke Ji a Jika a Dalilin Cire Tallafi

Ya ƙara da cewa tun a taron majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) da ya gabata, gwamnonin jihohi suka amince zasu goyi bayan sabon mafi ƙarancin albashi, rahoton Pulse ya tattaro.

Gwamnan Benue Ya Gana da Shettima Kan Batun Samar da Isasshen Abinci

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Benuwai ya gana da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a Aso Villa ranar Alhamis.

Gwamna Hyacinth Alia ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ba da fifiko wajen bunkasa harkar noma domin taimaka wa Najeriya ta samu wadatar abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262