Jamhuriyar Nijar Ta Katse Hulda da Najeriya Bayan Zaman Sulhu Ya Rushe
- Sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum a jamhuriyar Nijar sun yanke hulɗa da Najeriya bayan tattaunawar sansanci ta rushe
- Wannan mataki na zuwa ne awanni bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tura wakilai su gana da gwamnatin soji a Nijar
- Ƙungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin wa'adin mako ɗaya su maida Bazoum kan karagar mulki ko ta ɗauki matakin soji
Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta yanke hulda da Najeriya bayan kokarin da kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta yi na sasanta rikicin da ke faruwa ya ci tura.
Idan baku manta ba ƙungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar wa'adin mako ɗaya su maida shugaban ƙasa, Muhammed Bazoum kan kujerarsa.
Ƙungiyar ta buƙaci sojoji su maida Bazoum kan mulki kafin karewar wannan wa'adin ko kuma ta ɗauki matakin soji, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Amma shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya aika wata tawagar manyan mutane zuwa Nijar domin ganawa da shugabannin da suka yi juyin mulki, a ranar Alhamis.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai tawagar karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ta samu ganawa da wakilan gwamnatin mulkin sojin ne kawai, Dailypost ta rahoto.
Gwamnatin sojin Nijar ta yanke hulɗa da wasu ƙasashe
Bayan haka ne jamhuriyar Nijar ta sanar da yanke hulda da ƙasashen Najeriya, Togo, Faransa, mai mulkin mallaka, da kuma Amurka.
"Mun dakatar da ayyukan manyan jakadun Jamhuriyar Nijar a Faransa, Najeriya, Togo da Amurka," Gidan rediyon Faransa na kasa da kasa ya haƙaito ɗaya daga cikin sojin na sanarwa a gidan talabijin.
A ranar 26 ga watan Yuli, hambararren shugaban jamhuriyar Nijar, Bazoum ya shiga hannun jami'an tsaron fadar shugaban kasa, kuma a yammacin ranar, sojoji suka sanar da cewa sun kwace mulki.
Kwanaki biyu bayan hambarar da gwamnatin Bazoum, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya.
"Mun Shirya Zama Masu Shara a Villa" Miyetti Allah Ta Roki Tinubu Muƙamai
A wani rahoton Ƙungiyar Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN) ta roƙi shugaban ƙasa Tinubu ya waigo kan 'ya'yanta ya naɗa su muƙamai.
Shugaban kungiyar MACBAN na shiyyar Kudu maso Gabas, Allhaji Gidado Siddikki, ya ce wannan kiran da suka yi zuwa ga shugaba Tinubu ya zama dole.
Asali: Legit.ng