Mata Ta Maka Mahaifyarta A Kotu Don Sanin Hakikanin Mahaifinta A Abuja, Ta Ce Ta Gaji Da Gori

Mata Ta Maka Mahaifyarta A Kotu Don Sanin Hakikanin Mahaifinta A Abuja, Ta Ce Ta Gaji Da Gori

  • Rikita-rikita yayin da mata ta gurfanar da mahaifiyarta a gaban kotun Abuja don sanin wanene mahaifinta
  • Matar ta maka mahaifiyar tata ce a gaban kotun sauraran kararraki da ke yankin Bwari a birnin Abuja
  • Matar ta ce ta gaji da irin gori da kannenta su ke mata cewa mahaifinsu ba daya ba ne kuma ta bar musu gida

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Wata mata mai suna Hauwa'u Abubakar ta maka mahaifiyarta, Hajara Ibrahim a gaban kotu saboda ba ta taba sanin mahaifinta ba a birnin Tarayya Abuja.

Matar ta bayyana haka ne a gaban kotun yankin Bwari da ke Abuja a ranar Talata 1 ga watan Agusta bayan yawan gori da kannenta su ke mata.

'Ya ta maka mahaifiyarta a gaban kotu don sanin mahaifinta a Abuja
Hauwa'u Abubakar Ta Maka Mahaifyarta A Gaban Kotu Don Sanin Wanene Mahaifinta A Abuja. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Matar ta bukaci sanin mahaifinta a kotu

Ta ce ta je kotun ne saboda yadda kannenta da suke zaune tare ke mata gori cewa ta fita musu a gida ta je wurin mahaifinta, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Wani Mahaifi Ya Siyar Da Ransa Wurin Ceto Dansa Yayin Da Gini Ya Ruguje A Kansu, Matarsa Ta Yi Bayani

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce abin ya na ba ta mamaki ganin cewa a saninta duk mahaifinsu daya ne amma sai su ke nuna mata ita ba ‘yar cikin mahaifinsu ba ne.

Wacce ake kara, wato mahaifiyar matar ta gabatar da wani mai suna Abubakar Gani da ke zaune a Dutsen Alhaji da cewa shi ne mijinta na fari kuma mijin matar kafin su rabu.

Mahaifin nata ya musanta cewa shi ya haifeta

Sai dai a na shi martanin, mutumin ya ce shi bai san da wannan maganar ba, hasalima bai taba kusantar tsohuwar matar tasa ba, Aminiya ta tattaro.

Alkalin kotun, Abdurrahman Ibrahim, bayan sauraran korafe-korafen ya ba da umarnin a yi musu gwajin kwayar halittar gano asali wato DNA, don sanin gaskiyar al’amarin.

Alkalin ya kuma umarce su da su biya N200,000 kudin gwajin tare dage sauraran karar zuwa 8 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Rikici Yayin Da Wata Mai Koyon Sana’a Ta Tsere Da Jinjirin Uwar Dakinta Dan Kimanin Watanni 2 A Wurin Biki, An Bazama Nemanta

Magidanci Ya Garzaya Kotu Neman Datse Aurensa Da Matarsa, Kotu Tace Ba Aure A Tsakaninsu

A wani labarin, magidanci ya garzaya kotu tare da neman a datse igiyar aurensa da matarsa.

Magidancin mai suna Abayomi Oreyemi ya bukaci kotun da datse aurensa da matarsa mai suna Basirat Oreyemi kan zargin cin amana.

Ya ce akwai wani da matar ta ke dawo wa gida da shi mai suna Baba Aliya kuma ya taba lakada masa duka da ya yi magana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.