Nijar: Atiku Ya Ce Matakai Na Diflomasiyya Ya Kamata ECOWAS Ta Dauka Ba Na Soji Ba
- Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bayyana ra'ayinsa kan abinda ke faruwa a Nijar
- A wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta, ya nuna rashin goyon bayansa kan amfani da ƙarfin soji
- Atiku ya ce amfani da ƙarfin soji zai rura wutar rikicin, inda ya shawarci ECOWAS da bin matakai na diflomasiyya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Dan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana ra'ayinsa dangane da juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar.
Ya ce ba ya goyon bayan daukar matakai na soji da ECOWAS ke shirin yi wajen warware rikicin na jamhuriyar Nijar.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook da yammacin ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Atiku ya jinjinawa ECOWAS bisa tawagar sasanci da ta tura
Atiku ya jinjinawa ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), bisa ƙoƙarin da take yi na ganin an dawo da dimokuraɗiyya a ƙasar ta Nijar.
Atiku ya kuma shawarci ECOWAS da kar ta yi amfani da karfin soji akan waɗanda suka yi juyin mulkin, domin kuwa yin hakan na iya zafafa lamarin.
Ya ce rikicin da ke faruwa a Nijar abu ne da ke buƙatar matakai na diflomasiyya ba na nuna ƙarfi ba.
Da wuya tawagar ECOWAS ta iya dawo wa da Bazoum kujerarsa - Shehu Sani
Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan tsokacin da tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi dangane da zuwan tawagar ECOWAS Nijar.
Shehu Sani ya ce yana da yaƙinin cewa tawagar ta ECOWAS, za ta iya sanyawa a saki hamɓararren shugaban ƙasar Muhammad Bazoum, amma ba za ta iya sanya wa a maida masa da kujerarsa ba.
ACF ta shawarci ECOWAS kan matakin da take shirin ɗauka a Nijar
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan shawarar da ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta bai wa ECOWAS, na cewa kar ta yi amfani da matakai na soji a kan sojojin jamhuriyar Nijar.
Kungiyar ta ce Najeriya da Nijar sun kasance 'yan uwan juna ne tun tuni, a don haka take ganin matakan sasanci da sojojin da suka yi juyin mulkin ne ya fi dacewa.
Asali: Legit.ng