Juyin Mulkin Nijar: Kungiyar ACF Ta Shawarci Tinubu Kan Amfani Da Ƙarfin Soji
- Kungiyar ACF ta shawarci ECOWAS, kan matakin soji da take shirin ɗauka a kan Nijar
- Kungiyar ta ce yin sasanci da sojojin juyin mulkin na Nijar ne ya fi dacewa ba binsu ta ƙarfi ba
- Ya ce Najeriya da Nijar sun kasance 'yan uwan juna ne da ke da daɗaɗɗiyar alaƙa
Kungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta shawarci Bola Tinubu dangane da matakin da ya kamata ECOWAS da yake jagoranta ta ɗauka a kan jamhuriyar Nijar.
Kungiyar ta ce tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulkin ya fi dacewa ba amfani da ƙarfin soji ba kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren ƙungiyar ta ACF, Murtala Aliyu ya fitar ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ACF ta yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar
Aliyu ya ce ƙungiyar ta ACF ta bi sahun ƙungiyoyi irin su ECOWAS da AU, wajen yin Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli.
Kungiyar ta kuma yi kira ga jagoran juyin mulkin Abdoulrahame Tchiani, da ya yi gaggawar mayar da mulki hannun farar hula.
Sai dai Aliyu ya ce ƙungiyar ta ACF, ba ta goyon bayan amfani da ƙarfin soji da ƙasashen ECOWAS suka ce za su yi a kan sojojin na Nijar, idan suka ƙi mayar da mulki ga Bazoum kafin cikar wa'adin da ta ɗibar musu.
Najeriya da Nijar 'yan uwan juna ne
Ya bayyana cewa, tun tuni Najeriya da Nijar 'yan uwan juna ne da suka ƙulla alaƙa ta ɓangarori da dama da suka haɗa da auratayya, cinikayya da zamantakewa.
Haka nan ya ce, Najeriya ta yi iyaka da ƙasar ta Nijar da tsawonta ya haura sama da kilomita 1,500, sannan akwai gonaki da kasuwanni da 'yan ƙasar biyu ke amfani da su a tare.
A dalilin hakan ne ƙungiyar ta ACF ta ke ganin in aka ce za a yi amfani da ƙarfin soji a kan Nijar, za a shiga matsalolin da za su shafi har ita kanta Najeriyar.
Ya ce matakin na soji da ECOWAS ke shirin ɗauka zai iya yin amfani na ɗan lokaci, amma kuma illar da zai haifar za ta ɗauki zawon lokaci ba ta gushe ba kamar yadda yake a rahoton da Nigerian Tribune ta wallafa.
Shehu Sani ya yi hasashe kan sakamakon da tawagar ECOWAS za ta iya samu a Nijar
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan hasashen abubuwan da Shehu Sani yake ganin tawagar sasanci ta ECOWAS za ta iya cimmawa a zuwan da ta yi Nijar.
Tsohon sanatan ya ce babban abinda yake hasashen za a iya samu shi ne 'yancin hamɓararren shugaban daga hannun sojoji.
Asali: Legit.ng