Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kauyukan Neja, Sun Halaka Mutum 1 Tare Da Sace Fiye Da 50

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kauyukan Neja, Sun Halaka Mutum 1 Tare Da Sace Fiye Da 50

  • Tsageru sun hallaka wani tare da sace mutane fiye da 50 da suka hada da mata da yara kanana
  • ‘Yan bindigan sun sace wasu fiye da 20 da kuma shanu bayan hallaka wani mutum a Tsoho Kabula
  • Lamarin ya faru ne tsakanin Talata da Laraba duk a cikin wannan mako da muke ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Neja – ‘Yan bindiga sun hallaka mutum daya da kuma sace wasu fiye da 50 da suka hada da mata da yara a yankunan jihar Neja.

An kashe mutumin ne a yankin Tsoho Kabula da ke karamar hukumar Munya inda aka sace fiye da 20 da kuma sace shanu da dama.

'Yan bindiga sun halaka mutum 1 tare da sace fiye da 50 a jihar Neja
Jihar Neja Na Fama Da Hare-Haren Yan Bindiga Musamman A Yankunan Karkara. Hoto: Radio Nigeria.
Asali: Facebook

Lamarin ya faru ne tsakanin Talata zuwa Laraba a cikin wannan mako da muke ciki, Thisday ta tattaro.

Yadda 'yan bindigan suka kai hari a kauyukan jihar

Kara karanta wannan

Yan Sandan Kano Na Neman Wasu 'Yan Daba 3 Ruwa A Jallo, Za A Ba Da Kyautan Kudi Ga Wanda Ya Ba Da Bayani A Kansu

Hari na biyu ya faru a safiyar yau Alhamis 3 ga watan Agusta a yankin Girigori da ke karamar hukumar Rafi inda aka sace mutane 35 mafi yawansu mata da yara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya ta tattaro cewa hukumoni da ba a san su waye ba sun umarci ‘yan sa kai a yankin da ke ba da tsaro da su janye inda ko kwana daya ba a yi ba aka kawo mummunan hari a yankin, Akahi News ta tattaro.

Majiyar ta ce:

“Kasa da sa’o’i 24 bayan jami’an mu sun janye, ‘yan bindigan sun dawo tare da kai farmaki a kan mutane da ba za su iya kare kansu ba.”

An tabbatar cewa masu garkuwan ba su kira ‘yan uwan wadanda suka sacen ba don sanin matakin da za a dauka.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Gonan Sanata a Arewa, An Rasa Rai

Mutane na tserewa suna barin kauyukansu zuwa wasu wurare

Saboda yadda rashin tsaro ya tabarbare a yankunan, ‘yan kauye da dama na barin gidajensu zuwa wasu wurare da za su samu tsaro tare da barin gonakinsu.

Daya daga cikin wadanda suka kubuta daga hannun masu garkuwan ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan ba su kashe kowa ba.

Ya ce:

“Yan bindigan kawai sun sace mutane ne musamman mata da yara.”

Yayin hada wannan rahoto, sakataren din-din-din da ke kula da harkar tsaro, Alhaji Tariq Abdulkarim ya ce har zuwa wannan lokaci bai samu rahoton faruwar hakan ba.

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malaman Coci Biyu A Jihar Neja

A wani labarin, 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani limaman coci a Gyedna da ke Garam a karamar hukumar Tafa da ke jihar Neja.

An tabbatar da cewa maharan sun sace Fastocin guda 2, Fasto Paul Sanogo da Seminarian Melchior, a gidansu da ke Gyedna a yau Alhamis.

Kara karanta wannan

"Ba Su Mutunta Ni Ba": Wani Mutum Da Ya Rasa Aikinsa Ya Saki Matansa 3 Bayan Sun Ci Amanarsa

Mazauna yankin sun ce maharan sun yi ta harba bindiga na tsawon sa'o'i kafin suka sace Fastocin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.