Shugabar Alkalan da Ta Kafa Tarihin Aiki a Jihar Bayelsa Ta Kwanta Dama

Shugabar Alkalan da Ta Kafa Tarihin Aiki a Jihar Bayelsa Ta Kwanta Dama

  • Tsohuwar shugaban akalai a jihar Bayelsa, Kate Abiri CON, ta kwanta dama ranar Alhamis tana da shekaru 65 a duniya
  • Ma'aikatar shari'a ta jihar ta tabbatar da wannan babban rashi a wata sanarwa da ta fitar a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa
  • Gabanin rasuwarta, marigayyar ta kafa tarihin zama shugaban alkalan jiha da tafi daɗe wa a tarihi, ta rantsar da gwamnoni 4

Bayelsa - Tsohuwar shugabar alkalan da ta gabata a jihar Bayelsa, Mai shari'a Kate Abiri, ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 65 a duniya.

Babban rijistara a hedkwatar shari'a ta jihar Bayelsa, Mista Amaebi Orukari, shi ne ya sanar da wannan rashi a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Yenagoa.

Kate Abiri.
Shugaban Alkalan da Ya Kafa Tarihin Aiki a Jihar Bayelsa Ya Kwanta Dama Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A rahoton Daily Trust, Sanarwan ta ce:

"A madadin ɗaukacin ma'akatan sashin shari'a na jihar Bayelsa, Alkalin alkalai, mai shari'a Matilda Abrakasa Ayemieye na jimamin sanar da rasuwar mai shari'a Kate Abiri CON."

Kara karanta wannan

Tantance Ministoci: ‘Yar Katsina ta Sharba Kuka Gaban Sanatoci da Tuna Mahaifinta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ta rasu ne ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta, 2023 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a Asibitin Glory Land da ke Yenagoa a jihar Bayelsa. Kafin rasuwarta, ita ce shugabar Alkalan jiha da ta gabata."
"Ma’aikatar shari’a ta jihar Bayelsa zata yi kewar kokarinta a fannin fasahar sadarwa, bunkasa ababen more rayuwa, da gudummawar da take bai wa bangaren shari’a da jiha baki daya.”

A cewar sanarwar, za a sanar da lokacin jana'izarta a kan lokaci bayan kammala shirye-shirye da kuma tattaunawa da iyalan marigayya.

Taƙaitaccen tarihinta

Idan dai za a iya tunawa, Abiri ta yi ritaya daga ma'aikatar shari’a ta Bayelsa ne a ranar 13 ga watan Janairu bayan ta shafe shekaru 15 a matsayin babban alkalin alkalai kuma ta cika shekaru 65 na ritaya.

A lokacin da take aiki a matsayin babbar mai shari’a a jihar Bayelsa, Abiri ta rantsar da gwamnoni hudu a jihohin Bayelsa da Ribas, rahoton Allafrika ya tattaro.

Kara karanta wannan

Rudani Yayin Da Aka Kama Alkali Ya Yi Shigar Mata Yana Rubutawa Budurwarsa Jarrabawa, An Dauki Mataki A Kansa

Dirama a Majalisa Yayin da Ministar da Tinubu Ya Nada Ta Kauce Wa Tambaya Kan Mijinta

A wani rahoton kuma An yi wata 'yar dirama a majalisar dattawa ranar Larabar yayin da Dakta Doris Uzoka, daya daga cikin ministocin Tinubu ta tsallake wata tambaya kan mijinta.

Sanata Akpabio ya yi mata tambayoyi kan iyalinta amma yayin amsawa sai ta tsallake zancen miji, sanatoci suka kama dariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262