Yan Ta'addan Boko Haram Sun Yi Wa Masunta 8 Yankan Rago a Tafkin Chadi
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun halaka masunta a tsakanin iyakar Najeriya da Kamaaru a yankin tafkin Chadi
- Ƴan ta'addan na Boko Haram dai sun halaka masuntan ne sun takwas ta hanyar yi musu yankan rago
- Tsagerun ƴan ta'addan sun kuma sace wasu masuntan masu yawan gaske inda suka buƙaci a ba su maƙudan kuɗaɗen fansa
Jihar Borno - Ƴan ta'addan ƙungiyar Jama'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihad (Boko Haram) sun halaka masunta takwas a wani mummunan hari a jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun halaka ƴan ta'addan ne a yankin tafkin Chadi a tsakanin iyakar Najeriya da ƙasar Kamaru.
Ƴan ta'addan waɗanda ake zargin na ƙarƙashin Bakoura Buduma ne, sun farmaki masuntan ne a wani yanki kusa da tsibirin Kofi a Kamaru ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun haramta kamun kifi a iyakokin da ke ƙarƙashin ikon su bayan dakarun sojojin sama sun matsa musu da kai hare-hare ta sama, wanda hakan ya sanya da dama suka sheƙa barzahu ciki har da manyan kwamandojinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiyoyin sirri sun gayawa Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa ƴan ta'addan sun yi wa masuntan yankan rago ne.
Ƴan ta'addan dai sun zarge su ne da zama masu leƙen asiri da kuma tsallakawa zuwa iyakokin da suka haramta shiga.
Ƴan ta'addan sun kuma sace masunta masu yawa
Majiyoyin sun ƙara da cewa bayan halaka takwas daga cikin masuntan, ƴan ta'addan sun kuma sace da yawa daga cikinsu a cikin kwale-kwale guda takwas, sannan suka buƙaci da a ba su N5m kan kowane kwale-kwale da masuntan dake cikinsa.
Garkuwa da mutane, safarar makamai, satar shanu da sanya haraji kan manoma da masunta na ƙara yawaita a cikin ƴan kwanakin nan a yankin tafkin Chadi.
Ana zargin cewa ƴan ta'addan na son yin siyayya ne, musamman ta makamai da kayan haɗa bama-bamai.
Yan Ta'addan Boko Haram Sun Yanka Manoma a Borno
A wani labarin kuma, mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun halaka manoma 10 ta hangar yi musu yankan rago a jihar Borno.
Ƴan ta'addan dao sun bi manoman ne har cikin gonakinsu sannan suka aikata musu wannan mummunan ta'addancin.
Asali: Legit.ng