Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Gona Sanata a Jihar Kwara, Sun Halaka Manaja
- Wasu yan bindiga da ake kyautata zato masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan gonar tsohon Sanatan Kwara ta kudu
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun halaka Manajan da ke kula da gidan gonan kuma ɗan uwan tsohon Sanatan yayin harin na ranar Litinin
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda reshen jihar Kwara ya ce yanzu haka suna kan bincike
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kwara State - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe dan uwan tsohon Sanata mai wakiltar Kwara ta Kudu a majalisar dattawa, Simeon Suleiman Ajibola.
Marigayin, Biodun Ajibola, an ce shi ne manajan gidan gonar da yan bindigan suka kai hari, mallakar tsohon dan majalisar wanda ya fito daga karamar hukumar Ekiti a Kwara.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe 8:00 na safe.
An ce manajan gidan gonar ya rasa rayuwarsa ne yayin da ya yi ƙoƙarin guduwa daga hannun masu garkuwa da mutanen a yankin Isapa da ke ƙaramar hukimar Ekiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta ce yunkurin sace direban manajan, Felix Segun Adeleye, bai kai ga nasara ba bayan maharan sun maida hankali kan masu babura da suka nufo wajensu.
Majiyar ta ce:
“Sun bar Mista Adeleye, wanda ya samu rauni a kafa, suka bi masu babura. Duk da haka cikin ikon Allah Sanata Simeon Ajibola ba ya nan domin watakila da sun tafi da shi."
"Amma bisa rashin sa'a manajan ya gamu da ajalinsa yayin harin, direbansa kuma na kwance a wani Asibiti ana masa magani a Ilorin."
Wane mataki aka ɗauka kawo yanzu?
Sanata Ajibola ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Jaridar Leadership ta rahoto Sanatan na cewa:
“Yanzu da nake magana da ku ba na cikin kasar kuma ban san manufarsu ba. Na bukaci ‘yan sanda da su yi cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin."
Da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya bayyana cewa jami'ansu na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Hafsoshin Tsaron Kasahen Afirka Sun Sa Labule a Abuja Kan Juyin Mulkin Nijar
A wani rahoton kuma Hafsoshin tsaron ƙasashen yammacin Afirka na gana wa a hedkwatar tsaro da ke Abuja kan juyin mulkin da ya auku a jamhuriyar Nijar.
Taron na gudana ƙarƙashin jagorancin shugaban hafsoshin tsaron ƙungiyar ECOWAS kuma babban hafsan tsaron Najeriya, Christopher Musa.
Asali: Legit.ng