Majalisar Dattawa Ta Dauki Mataki Kan Masu Zanga-Zangar Da Suka Kutsa Cikin Harabarta
- Mambobin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) sun fara zanga-zanga bisa cire tallafin man fetur, inda wasu masu zanga-zanga suka kutsa majalisar tarayya
- Masu zanga-zangar sun taru a Abuja, Legas da wasu sauran sassan ƙasar nan domin nuna ɓacin ransu kan halin da ake ciki a ƙasa
- A ranar Laraba da ta gabata, ƙungiyar NLC ta ba gwamnatin tarayya wa'adin kwana bakwai ta sauya tsare-tsare takurawa talaka da ka fito da su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Majalisar dattawa a ranar Laraba, 2 ga watan Yuli, ta kafa kwamitin da zai tattauna da ƙungiyoyin ƙwadago dake zanga-zanga waɗanda suka karya ƙofar shiga majalisar ta farko.
Masu zanga-zangar dai sun faro ne daga shatale-talen Fountain a birnin tarayya Abuja zuwa majalisar tarayya kan abinda suka kira "tsauraran matakan tattalin arziki" na gwamnati Shugaba Bola Ahmed Tinubu, cewar rahoton Channels tv.
Majalisar ta tattauna da fusatattun masu zanga-zanga bayan karya ƙofar majalisa
Bayan sun isa majalisar tarayya, masu zanga-zangar sun karya ƙofar farko ta majalisar sannan suka shige zuwa cikin harabar majalisar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya shiga ganawa sanatoci a keɓance, inda bayan ya fito daga taron ya bayyana cewa majalisar ta kafa wani kwamiti mai mutum uku domin tattaunawa da masu zanga-zangar.
Kwamitin zai kasance ƙarƙasin jagorancin mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Ali Ndume, sanatan Borno ta Yamma.
Majalisar ta kuma cimma matsaya cewa nan bada daɗewa ba za ta gana da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon domin samar da mafita kan halin da ake ciki
Ndume tare da sauran sanatocin guda biyu, Sanata Ireti Kingibe da Sanata Tony Nwonye sun gana masu zanga-zangar a majalisar tarayya.
Da yake magana da masu zanga-zangar, Sanata Ndume ya buƙaci ƙungiyoyin ƙwadagon da su janye zanga-zangar gama garin da su ke yi a faɗin ƙasar, sannan su ba majalisar sati ɗaya domin ta magance buƙatun da suka gabatar, rahoton The Punch ya tabbatar.
Masu Zanga-Zanga Sun Kutsa Majalisar Tarayya
Da zu rahoto ya zo cewa masu zanga-zanga sun kutsa kai cikin harabar majalisar tarayya a yayin da su ke gudanar da zanga-zangar nuna adawa da cire tallafin man fetur.
Masu zanga-zangar sun kutsa kai ne cikin majalisar da ƙarfin tuwo ta hanyar karya ƙofar shiga majalisar.
Asali: Legit.ng