Masu Zanga-Zanga Sun Karya Kofar Shiga Majalisar Tarayya
- Masu gudanar da zanga-zanga sun kutsa da ƙarfin tuwo cikin harabar majalisar tarayya a birnin tarayya Abuja
- Masu zanga-zangar sun kutsa cikin majalisar ne bayan sun karya ƙofar shiga harabar majalisar domin gudanar da zanga-zanga
- Ƙungiyar ƙwadago dai ta fara gudanar da zanga-zangar gama gari domin adawa da abinda ta kira tsauraran matakan tattalin arziƙi na Tinubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Masu gudanar da zanga-zanga kan abinda suka kira "tsauraran matakan tattalin arziƙi" na shugaba Tinubu, sun kutsa kai cikin majalisar tarayya a birnin tarayya Abuja.
Masu zanga-zangar dai sun kutsa kai cikin harabar majalisar ne bayan sun karya ƙofar shiga majalisar, Channels tv ta yi rahoto.
Tun da farko masu zanga-zangar a ƙarƙashin shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago Joe Ajaero na NLC da Festus Osifo na TUC, sun buƙaci jami'an tsaron dake a majalisar da su buɗe musu ƙofar domin shiga ciki su nuna ɓacin ransu.
Bayan jami'an tsaron sun ƙi buɗe musu ƙofar shiga majalisar, fusatattun masu zanga-zangar sun karya ƙofar da ƙarfin tsiya inda suka kutsa kai cikin harabar majalisar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A yau Laraba ne dai ƙungiyoyin ƙwadago an NLC da TUC da sauran takwarorinsu suka fara gudanar da zanga-zanga a birnin tarayya Abuja da wasu jihohi da suka haɗa da Legas, Abia, Plateau, Kaduna, Kano, Rivers, Zamfara, Katsina, Cross River, Ebonyi, Enugu, Kwara, Ogun, Imo, Ondo, da Edo.
Ba gudu ba ja da baya dangane da zanga-zanga, Ajaero
Tun da farko, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, Joe Ajaero, ya bayyana cewa babu abinda zai hana gudanar da zanga-zangar ko da gwamnati ba ta so hakan ba.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ba za ta fasa zanga-zangar ba har sai idan ta samu tabbaci mai kyau daga wajen gwamnati.
Ajaero ya bayyana cewa haɗin kan da suka daga ɓangaren jihohi shi ne zai nuna ko zanga-zangar za ta ci gaba daga yau, gobe ko har sai abinda ya turewa buzu naɗi.
"Mun zo nan ne domin gudanar da zanga-zanga, da bayyana cewa tun lokacin da mu ka fara tattaunawa babu abinda ya zo hannunmu." A cewarsa.
An Fatattaki Masu Zanga-Zanga a Kano
A wani labarin kuma, ƴan sanda sun fatattaki mutanen da suka yi sammakon fitowa domin gudanar da zanga-zanga a birnin Kano.
Mutanen sun fito ne domin halartar zanga-zangar da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta shirya domin yin Allah wadai da tsare-tsaren gwamnati.
Asali: Legit.ng