Zamu Take Ku Kamar Kiyashi, Fani-Kayode Ya Gargadi Sojojin Burkina Faso, Mali Da Na Nijar
- Jigon APC Femi Fani-Kayode ya gargaɗi sojojin Nijar, Mali da Burkina Faso daga yin faɗa da Najeriya
- Ya ce Najeriya ba kanwar lasa ba ce domin kuwa za ta mutsuttsuke sojojin waɗannan ƙasashen idan akwai gwaza yaƙi
- Fani-Kayode ya kuma ce har yanzu wata ƙasa ba ta taɓa cin sojojin Najeriya da yaƙi ba a filin daga
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jigo a jam'iyyar APC Femi Fani-Kayode ya aika da zazzafan martani ga sojojin Burkina Faso, Mali da na Nijar.
Ya ce idan suka yarda suka gwabza yaƙi da Najeriya, to lallai za su kwashi kashinsu a hannu.
Ya aika da wannan saƙon gargaɗin ne ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata, 1 ga watan Agustan da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya
Kar a raina sojojin Najeriya duk da ƙalubalen da suke fuskanta
Fani-Kayode ya bayyana cewa, sojojin Najeriya ba kanwar lasa ba ne duk da ƙalubalen da su ke fuskanta a gida na yaƙi da 'yan ta'adda.
Ya ce idan aka fita filin daga domin gwabza yaƙi gaba da gaba, har yanzu ba a taɓa cin nasara a kan sojojin Najeriya ba.
Ya kuma ce shugabannin ƙasashen Mali da Burkina Faso ba su da lissafi kuma suna ƙoƙarin yin barazana ta rashin lissafi.
Ya ƙara da cewa babban kuskuren da sojojin ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar za su yi shi ne raina ƙarfin sojin Najeriya.
Yi wa Najeriya barazanar yaƙi ba ci ba ne
Fani-Kayode ya kuma ce Najeriya na da sauƙin fushi, amma idan sojojin Burkina Faso, Mali da na Nijar suka kai ta bango, to lallai za su gane kurensu.
Ya ƙara da cewa yi wa Najeriya barazana da yaƙi ba ƙaramin abu ba ne, wanda idan hakan ta faru, lallai za su ɗanɗana kuɗarsu.
A kalamansa:
“A sauƙaƙe za mu mutsuttsuke su kamar kiyasai da ƙafarmu mu mayar da su can inda suka baro.”
Kasashe 6 da ke ƙarƙashin mulkin soja a ƙasashen Afrika
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan ƙasashen Afrika shida da ke a ƙarƙashin mulkin soja a halin da ake ciki.
Ƙasashen da ke a ƙarƙashin mulkin soja a ƙasashen Afrika sun haɗa da Nijar, Mali da ƙasar Burkina Faso.
Asali: Legit.ng