Kungiyar NLC Ta Magantu Kan Yuwuwar Janye Zanga-Zangar da Ta Shirya a Najeriya
- Ƙungiyoyin kwadugo sun bayyana cewa za su zauna domin duba yuwuwar haƙura da shiga yajin aiki da zanga-zangar da suka shirya
- A gobe Laraba, 2 ga watan Agusta, NLC da sauran ƙawayenta suka shirya fara yajin aikin gama gari kan tsadar fetur
- Sai dai bayan tattauna wa da wakilan shugaban ƙasa a Aso Villa, NLC da TUC sun ce zasu sake tattauna wa a tsakaninsu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Ƙungiyoyin kwadugo da suka ƙunshi NLC da TUC sun bayyana cewa da yuwuwar su haƙura su janye gagarumin yajin aikin gama gari da zanga-zanga da suka shirya fara wa gobe Laraba.
Sakataren kungiyar NLC ta ƙasa, Emma Ugbaja, ne ya faɗi haka yayin zanta wa da masu ɗauko rahoto a fadar shugaban ƙasa, ranar Talata, 1 ga watan Agusta, 2023.
Ya nuna alamun zasu iya janye shirinsu ne jim kaɗan bayan fitowa daga ganawar wakilan NLC da kwamitin raba tallafi na shugaban ƙasa wanda ya gudana a Aso Villa, Abuja.
Sakataren NLC ya ce duk da ana murna da maraba da matakan sauƙaƙa wa yan Najeriya da shugaba Bola Tinubu ya bayyana a jawabin kai tsaye, amma ƙungiyar kwadugo na ganin basu wadatar ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ugbaja ya ce kungiyar za ta tuntubi mambobin da take wakilta domin cimma matsaya kan mataki na gaba kafin ranar yau ta kare, Daily Trust ta rahoto.
Zamu gana yau da yamma dom ɗaukar matsaya - TUC
A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar 'yan kasuwa (TUC) na ƙasa, Festus Osifo, ya ce:
"A bangaren gwamnati, ka tambayi wani abu game da zanga-zangar da muka shirya, eh sun nemi mu ajiye zanga-zangar."
"Amsar da muka ba su ita ce, za mu koma da yammacin yau mu tattauna a tsakanin mu kan batun, kuma za ku ji ta bakinmu a karshen wannan tattaunawar."
Muna fatan zasu janye - Gbaja
A rahoton jaridar The Cable, Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya bayyana kungiyar kwadago a matsayin kungiya mai “sauraro.”
Ya ce suna fatan ƙungiyar ba za ta gudanar da zanga-zangar da ta shirya ba bayan sauraron jawabin shugaba Tinubu kai tsaye, wanda ya yi wa al’ummar kasar ranar Litinin.
FG Zata Raba Wa Mutane Sama da Miliyan 1 Tallafin N50k Kowanensu, Tinubu
A wani rahoton kuma Tinubu ya yi alƙawarin cewa FG zata raba tallafin N50k ga kowane ɗaya daga cikin masu kanana da matsakaitan sana'o'i 1,300 a kowace ƙaramar hukuma.
Shugaban ƙasar ya sanar da cewa gwamnatinsa ta ware biliyan N50bn domin tallafawa kananan yan kasuwa a faɗin ƙananan hukumomin Najeriya 774.
"Shugaba Tinubu Ba Zai Yi Dana Sanin Nada Ni Minista Ba", Jawabin Wike Yayin Tantance Shi a Majalisa
Asali: Legit.ng