Gwamnan Kwara Ya Amince a Bai Wa Kowane Dalibin Jiharsa N10,000
- Gwamnan jihar Kwara ya umarci a raba wa dalibai haifaffun jiharsa tallafin N10,000 domin rage raɗadin cire tallafi
- A wata sanarwa da sakatarensa ya fitar ranar Talata, gwamnan ya bayyana yadda kowane ɗalibi zai cike bayanansa don samun tallafin
- Ya kuma amince da a biya wasu rukunin jami'an tsaro ƙarin N10,000 duk a wani bangare na taimaka wa al'ummar jihar Kwara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kwara State - Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya umarci a bai wa kowane ɗalibin jihar kyautar N10,000 domin rage radaɗin cire tallafin man fetur.
Sakataren watsa labaran mai girma gwamna (CPS), Rafiu Ajakaye, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Talata, 1 ga watan Agusta, 2023.
Haka zalika gwamna Abdulrazaq ya amince da rabba tallafin N10,000 ga wasu rukunonin jami'an tsaro, waɗanda ya kira da na sahun farko wajen tabbatar da tsaro.
Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa dukkan waɗanda tagomashin ya shafa zasu karɓi tallafin ta hannun ofishin Kwara State Social Investment Programme (KWASSIP).
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan tallafin ɗaliban da gwamnan ya amince da shi na lokaci ɗaya ne kawai, kuma hanya ce ta fita daga tsarin tallafin ƙaratun Busary, wanda ya shafi ɗaliban ajin ƙarshe a manyan makarantu kaɗai.
Gwamnan ya kuma ƙara yawan adadin tallafin karatu na musamman ga ɗaliban ajin karshe daga N5,000 da aka shafe tsawon lokaci, zuwa N10,000 ga kowane ɗalibi.
Matakan da ɗalibai zasu bi domin cin gajiyar tallafin
Sanarwan ta ce:
"Gwamnati ta kafa kwamitin da zai sa ido kan bada wannan tallafi karkashin jagorancin shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar Kwara (KWSUBEB), Farfesa Shehu Raheem Adaramaja."
"Sauran yan kwamitin sun haɗa da wasu jami'an ma'aikatar kula da manyan makarantu, sashin harkokin kuɗi, ma'aikatar kuɗi da kuma wakilin kungiyar ɗaliban Kwara (NAKSS) da ta ƙasa NANS."
"Kwamitin zai buɗe shafin yanar gizo, duk ɗalibin da ya cancanta da samun tallafin ya shiga ya cike bayanan da ake buƙata."
Shugaba Bola Tinubu Ya Sanar da Sabon Tallafi Ga Daliban Najeriya
A wani rahoton kuma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da raba wa manyan makarantun gaba da sakandire motocin zirga-zirgar ɗalibai.
Hakan na cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a shafinta na sada zumunta ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, 2023.
Asali: Legit.ng