Rashin Ciniki Ya Sanya 'Yan Kasuwar Man Fetur Siyar Da Gidajen Mai, Cewar IPMAN
- Cire tallafin man fetur da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, ya jefa ƴan kasuwar man fetur cikin wani mawuyacin hali
- Ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN) ta bayyana cewa mambobinta da dama a sassan ƙasar nan sun sanya gidajen man su a kasuwa saboda rashin ciniki
- Shugaban ƙungiyar ya kuma koka kan yadda wasu hukumomin gwamnatin tarayya suka riƙe wa mambobin ƙungiyar makuɗan kuɗaɗe
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN) ta bayyana cewa kasuwancin mambobinta ya shiga cikin garari tun bayan da aka tsige tallafin man fetur.
Jaridar Daily Trust tace shugaban ƙungiyar na ƙasa, Chinedu Okoronkwo, shi ne ya bayyana hakan a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai wanda ke bincike kan ƙarin kuɗin man fetur da aka yi kwanan nan a ranar Talata, 1 ga watan Agustan 2023.
A cewarsa, a birnin Ibadan na jihar Oyo kaɗai sama da mambobin ƙungiyar 40 ne suka sanya gidajen man su a kasuwa, inda ya ƙara da cewa da yawa daga cikin mambobin ƙungiyar a sauran sassan ƙasar nan, na yin hakan saboda yadda ciniki ya yi baya sosai.
Cinikin man fetur ya yi baya sosai
Ya bayyana cewa ƴan kasuwan da su ke siyar da babbar mota mai ɗaya a cikin kwana uku, yanzu sai ta yi wata sannan take ƙarewa, cewar rahoton Nairaland.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Okoronkwo ya bayyana cewa ana siyo babbar motar mai kan N25m, wanda a ciki ko ribar N500,000 ba a samu, inda ya ƙara da cewa abinda ake samun ya yi kaɗan ya biya albashin ma'aikata da sauran buƙatu irinsu kuɗin haraji.
Shugaban na IPMAN ya koka cewa hukumomin PEF da NNPCL sun riƙe wa ƙungiyar kuɗaɗen mambobinta da suka kai N750bn.
A cewar shugaban, yayin da PEF ta tiƙe N250bn, NNPCL tana riƙe da N500bn.
Hanyoyin Magance Tsadar Man Fetur, IPMAN
A wani labarin kuma, ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN) ta bayyana hanyoyin da za a bi domin magance tashin farashin man fetur a ƙasar nan.
Ƙungiyar ta bayyana cewa tace man fetur a cikin gida Najeriya, shi ne babbar hanyar da za ta sanya farashinsa ya yi ƙasa a kasuwa.
Asali: Legit.ng