Hukumar Kula Da Asibitocin Kano Ta Sallami CMDs 3, Ta Dakatar Da Likitoci Da Malaman Jinya
- An kori manyan jami'an lafiyar wasu asibitocin gwamnati uku da ke jihar Kano
- Babban sakataren Hukumar Kula da Asibitoci ta jihar Kano Dakta Mansur Nagoda ne ya bayyana hakan
- Haka nan hukumar ta sanar da dakatar da likitoci da malaman jinya na asibitocin uku da abin ya shafa
Kano - Babban sakataren Hukumar Kula da Asibitoci (HMB), ta Jihar Kano, Dakta Mansur Nagoda, ya amince da korar manyan jami’an lafiya na wasu asibitoci uku da ke jihar.
Asibitocin da abin ya shafa su ne Babban Asibitin Imam Wali, Abubakar Imam Urology Center da kuma asibitin haihuwa na Nuhu Bamalli kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar, Samira Sulaiman ta fitar kuma ta bayyanawa manema labarai a daren ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dakatar da duka likitoci da malaman jinya suka yi aiki a ranar Lahadi
Haka nan kuma, Nagoda ya amince da dakatar da duka likitoci da ma'aikatan jinyan da ke aikin yamma na ranar Lahadi, 30 ga Yulin shekarar 2023.
Ya ce wannan mataki ya zama dole domin hukunta ma'aikatan lafiyar saboda sakaci da suke yi da ayyukansu.
Ya kara da cewa, sukan bar aikin kula da marasa lafiya da aka kawo asibitocin a hannun daliban da suka zo koyon aiki, maimakon su tsaya su kula da su da kansu.
Hukumar ba za ta lamunci wasa da aiki ba
Nagoda ya kuma bayyana cewa hukumar kula da asibitocin ba za ta lamunci sakaci da aiki da duk wani malamin lafiya ke yi ba kamar yadda Kano Focus ta wallafa.
Ya ce ba za su lamunci zuwa aiki a makare ba, ko barin wurin aiki ba bisa ka'ida ba da wasu ma'aikatan ke yi, inda ya bayyana cewa duk wanda aka kama yana aikata hakan, zai fuskanci hukunci daidai da abinda dokar ma'aikata ta tanada.
Daga karshe Nagoda ya kuma yi kira ga sauran asibitocin da su kara kaimi kan ayyukansu, domin hukumar za ta ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da ayyuka domin farfado da fannin lafiya a jihar.
Cutar 'Diptheria' ta kwantar da mutane 130 a asibiti a jihar Kano
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton sake bullar cutar nan ta mashako wacce ake kira da 'diptheria' a jihar Kano.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Abubakar Yusuf a zantawarsa da manema labarai, ya bayyana cewa akalla mutane 130 ne aka kwantar a asibiti sakamakon kamuwa da suka yi da cutar.
Asali: Legit.ng