Shugaba Bola Tinubu Ya Sanar da Sabon Tallafi Ga Daliban Najeriya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da raba wa manyan makarantun gaba da sakandire motocin zirga-zirgar ɗalibai
- Hakan na cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a shafinta na sada zumunta ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, 2023
- Ta ce matakin na ɗaya daga cikin kudirorin shugaban ƙasa na ganin ɗalibai suna kai kawo a makarantunsu ba tare da shan wahala ba
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da sabon tallafin da gwamnatinsa ta ware wa ɗaliban manyan makarantun gaba da sakandire.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta wallafa a shafinta na dandalin Tuwita ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, 2023.
Sanarwan ta ce shugaba Tinubu ya bada umarnin raba motocin Bas-Bas ga jami'o'i, kwalejojin fasa da kwalin ilimin da ke sassan ƙasar nan baki ɗaya.
Fadar shugaban ƙasan ta kara da cewa shugaba Tinubu ya amince da wannan matakin ne domin tabbatar da cewa dukkan ɗalibai na samun damar zuwa azuzuwan karatu da ɗakunan kwanansu kyauta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Meyaaa Tinubu ya ɗauki wannan matakin?
Sanarwan ta ce:
"Shugaba ƙasa Tinubu ya amince da samar da motocin bas ga ƙungiyoyi. dalibai na dukkanin Jami'o'i, kwalejin fasaha da Kwalejojin Ilimi a fadin kasar."
Burin shugaban kasa shine ya ga dalibai suna iya zuwa wuraren karatu su ba tare da wahala ba sakamakon tsadar kudin sufuri."
"Samar da motocin bas din zai kuma kawar da nauye-nauyen ƙarin ɗawainiyar yau da kullun ga iyaye da masu kula da ɗalibai."
Wannan na zuwa ne makonni bayan shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar bai wa ɗaliban Najeriya bashi domin su cimma burinsu na yin karatu ba tare da samun tnagarɗa ba.
Yanzu-Yanzu: "Mun Tara Sama da N1tr" Shugaba Tinubu Ya Tona Kuɗin Da Ya Ƙwato Bayan Cire Tallafin Fetur
Dokar zata bai wa ɗalibai damar karɓan rance Kuɗi daga gwamnatin tarayya domin ƙarisa karatu amma zasu biya a hankali a hankali.
Shugaba Bola Tinubu Ya Nada Tsohon Hadimin Osinbajo a Matsayin Kakakinsa
A wani rahoton na daban kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin midiya da yaɗa labarai.
Tinubu ya naɗa Ajuri Ngelale, tsohon hadimin tsohon mataimakin.shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo a matsayin kakakinsa.
Asali: Legit.ng