Gwamna Sanwo Olu Ya Fara Tallafawa Mutanen Legas Don Rage Radadin Cire Tallafi

Gwamna Sanwo Olu Ya Fara Tallafawa Mutanen Legas Don Rage Radadin Cire Tallafi

  • Gwamnan jihar Legas ya bayyana matakan tallafi da gwamnatinsa ta ɗauka domin rage wa al'ummar jihar zafin cire tallafin fetur
  • Babajide Sanwo-Olu ya umarci a rage kuɗin motar Bas mallakin gwamnati da kaso 50 cikin 100 daga ranar Laraba
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa tallafin mai ya tafi, lamarin ya jawo tsadar kayayyaki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos state - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya sanar da daukar matakan dakile tasiri da raɗaɗin cire tallafin man fetur wanda gwamnatin tarayya ta yi.

A shafinsa na Tuwita, Sanwo-Olu ya jero tallafi da kuma matakan da gwamnantinsa ta ɗauka domin sauƙaƙa wa talakawa halin ƙuncin rayuwa da suka shiga bayan cire tallafin mai.

Gwamna Babajide Sanwo Olu na jihar Legas.
Gwamna Sanwo Olu Ya Fara Tallafawa Mutanen Legas Don Rage Radadin Cire Tallafi Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Twitter

Sanwo-Olu na jam'iyyar APC ya kaddamar da bada tallafin ne a wurin taron manema labarai ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ba Zai Yi Dana Sanin Nada Ni Minista Ba", Jawabin Wike Yayin Tantance Shi a Majalisa

Wane matakai gwamnan jigar Legas ya ɗauka?

Da yake jawabi, gwamnan ya ba da umarnin rage kashi 50 cikin 100 na kudin sufurin motocin bas mallakin gwamnatin jihar daga ranar Laraba mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika Babajide Sanwo Olu ya buƙaci a rage kashi 25 cikin 100 na kuɗin sufurin motocin bas masu launin rawaya, waɗanda aka fi sani da "Danfo."

Gwamnan ya kuma ba da umarnin samar da karin motocin bas ga ma’aikatan gwamnati da kuma raba kayayyakin abinci ga talakawa da iyalai marasa galihu.

A wata sanrwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, gwamnan Legas ya ce:

"Na fahimci damuwa da ƙalubalen da mutane ke fuskanta a waɗannan lokuttan na kawo sauyi. Dangane da illolin cire tallafin man fetur, na ɗauki wasu matakan farfaɗo da tattalin arziki da jin ƙai."

Kara karanta wannan

Tausayin talaka: Zulum da wasu gwamnoni 2 sun kawo hanyar rage radadin cire tallafi

"Daga ranar Laraba, zamu fara aiwatar da ragin kashi 50% na kuɗin Bas na Legas, domin saukaka wa matafiya a fadin birnin. Tare da haɗin guiwar ƙungiyoyi, za a rage ƙaso 25% na motocin Bas (Damfo)."

Majalisar Dattawa Ta Ɗauki Matsaya Kan Ministan da Ya Fara Firamare Yana Shekara 3

A wani rahoton kuma Ministan da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa daga jihar Benuwai ya haddasa ruɗani da kace-nace a majalisar dattawa.

Yayin tantance shi ranar Litinin, Farfesa Utsev ya faɗa wa majalisa cewa an haife shi a 1980 kuma ya fara karatun Firamare a 1984.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262