Mai Koyon Sana’a Ta Tsere Da Jinjiri Dan Wata 2 A Wurin Bikin Yaye Dalibai A Kwara
- Jimami yayin da ‘yar aiki ta sace jariri mai kimanin watanni biyu na uwar dakinta a birin Ilorin na jihar Kwara yayin wani biki
- An sace jaririn ne mai suna Usman Idris yayin bikin kammala karatun dalibai bayan ‘yar aikin ta karbe shi da niyyar taimako
- Mahaifiyar jaririn, Sekinat ta ce makwanni biyu da suka wuce Iya Ibeji ta zo wurinta da cewar tan a son koyan sana'a
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kwara - An sace wani jariri mai kimanin watanni biyu daga mahaifyarsa yayin bikin yaye dalibai a wata makaranta a birnin Ilorin na jihar Kwara.
Jaririn mai suna Usman Idris an sace shi ne da misalign karfe 3:00 na yammaa ranar Asabar 29 ga watan Yuli yayin bikin a harabar makarantar da ke Deeper Life Sawmill a Ilorin.
Wata daga cikin iyaye da ta nemi a boye sunanta ta tabbatarwa Daily Trust cewa matar ta bukaci tashi ne sai wata ‘yar aiki ta karbi jaririn don taimaka mata.
Mahaifiyar jarirn ta bayyana yadda aka sace yaron
Mahaifiyar jaririn mai suna Sekinah da aka fi sani da Iya Mujidat ta tabbatar da faruwar hakan a ranar Lahadi 30 ga watan Yuli.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ta ce abin da ya faru ya dugunzuma iyalansu gaba daya, inda ta bayyana wacce ake zargin da fara kuma doguwa da ke sanye da shudin atamfa da kuma bakin dan kwali, cewar The Nation.
A cewarta:
“Ta zo wuri na makwanni biyu da suka wuce ta ce tana son koyan yadda ake kuli-kuli, na amince ba tare da sanin gidansu ba kuma bani da lambar wayarta.
“Mun je wurin bikin kammala karatun tare kuma ta bukaci ta rike min jariri lokacin da na raka dan uwana karbar shaidar kammala karatu.
“Aikin Nan Akwai Hatsari Sosai”: Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu
“Wannan shi ne karshen ganinta da na yi, mun kai rahoto ofishin ‘yan sanda na yanki a Surulere da ke Ilorin amma har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.”
'Yan sanda sun koka kan yadda matar ta yi sakaci wurin amincewa da 'yar aikin
Daya daga cikin ‘yan sandan ya koka kan yadda mutum zai dauki ‘yar aiki har tsawon makwanni biyu ba tare da yasan ‘yan uwanta ba da kuma kwakkwaran bincike ba.
Har lokacin tattara wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi bai dauki wayar da ake kiran shi ba.
Mutane Sun Dimauta Yayin Da Aka Tsinci Jariri Kwance Cikin Tsumma a Jihar Kaduna
A wani labarin, mutane sun shiga damuwa yayin da aka tsinci jarir a cikin tsumma a unguwar Mu'azu da ke birnin Kaduna.
An tsinci jaririn ne a ranar Asabar 17 ga watan Yuni da misalin karfe takwas na safiyar ranar.
Jaririn an tsince shi ne a wani kangon da ba a karasa ba yayin da wani matashi ya yi ta maza ya dauke shi zuwa wurin 'yan sa kai a yankin.
Asali: Legit.ng