Emefiele: Peter Obi Ya Yi Magana Kan Takaddamar Jami'an DSS Da Na Gidan Yari a Kotu

Emefiele: Peter Obi Ya Yi Magana Kan Takaddamar Jami'an DSS Da Na Gidan Yari a Kotu

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya caccaki halayyar da jami'an DSS da na NCoS suka nuna a wajen shari'ar Godwin Emefiele
  • A wajen shari'ar Emefiele, jami'an hukumomin biyu sun ba hammata iska kan wanda zai tafi da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya
  • Obi ya bayyana cewa ya yi mamakin abubuwan dake faruwa a Najeriya, inda ya nuna cewa abin da ya faru ya nuna yakamata a samu sabuwar Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi martani kan taƙaddamar da aka yi a tsakanin jami'an hukumar DSS da na hukumar gidajen yarin Najeriya (NCoS) a wajen shari'ar Godwin Emefiele.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin takaici cewa jami'an hukumomin za su zubar da ƙima haka.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: An Faɗi Sunan Wanda NEC Ke Shirin Naɗa Wa a Matsayin Shugaban APC Na Ƙasa Ranar Alhamis

Peter Obi ya yi magana kan takaddamar DSS da NCoS kan Emefiele
Emefiele yana fuskantar tuhumar mallakar makamai a kotu Hoto: Peter Obi/Ibrahim Mansur
Asali: Twitter

Obi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 26 ga watan Yuli a lokacin wata tattaunawa #PeterObiOnParallelFacts a Twitter, wacce The Parallel Facts ta shirya wacce Legit.ng ta saurara.

"Bana magana da yawun hukumomin tsaron, bana magana da yawun Emefiele amma abubuwan dake faruwa a Najeriya suna bani mamaki." A cewarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Obi ya buƙaci sanin meyasa ake tuhumar Emefiele duk da cewa gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ce ta naɗa shi kan muƙami.

Ya bayyana cewa gwamnatin ita ce kuma ta sake sabunta naɗin Emefiele, amma yanzu ta koma hantararsa duk da lambar yabo ta ƙasa mafi daraja ta uku (CFR) da ta ba shi.

Peter Obi ya yi kiran a samar da sabuwar Najeriya

Obi ya bayyana cewa shari'ar Emefiele shaida ce cewa akwai buƙatar sabuwar Najeriya wacce ake bin doka da oda.

Kara karanta wannan

Ko Ganduje Zai Zama Shugaba? Jam'iyyar APC Ta Sanaya Ranakun Manyan Tarukanta 2

An gurfanar da Emefiele a ranar Talata, 25 ga watan Yuli inda kotu ta bayar da belinsa kan N20m, inda alƙalin kotun ya yanke cewa a sakaya shi a gidan gyaran hali na Ikoyi har zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗan belinsa.

Bayan an kammala shari'ar Emefiele ta ranar, jami'an DSS sun haƙiƙance sai sun tafi da Emefiele saɓanin umarnin da kotun ta bayar.

Hakan shi ne ya kawo jami'an hukumomin biyu suka ba hammata iska.

Charly Boy Ya Sha Alwashi Kan Peter Obi

Rahoto ya zo cewa ɗaga daga cikin magoya bayan Peter Obi kuma mawaƙi a Najeriya, Charles Oputa, ya sha babban alwashi kan ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iƴyar Labour Party (LP).

Charly Boy ya yi alƙawarin tafiya tumbur haihuwar uwarsa idan Peter Obi ya yi nasara a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, domin nuna murnarsa akan hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng