Cire Tallafin Man Fetur: Borno, Adamawa da Yobe, Sun Rage Radadin Cire Tallafi Ga Ma’aikata da Dalibai
- Yayin da tsadar rayuwa ke kara kamari, gwamnatin jihohin Arewa maso Gabas sun dauki matakin dakile radadi
- An ruwaito yadda gwamnatocin Yobe, Borno da Adamawa ke kokarin rage wa jama’a kudaden sufuri a jihohinsu
- Hakazalika, gwamnatin Adamawa za ta fara ba da karin N10000 kan albashin ma’aikata da kuma masu karbar fansho
Arewa maso Gabas - Gwamnatocin jihohin Borno da Adamawa da Yobe sun fara daukar matakan dakile radadin hauhawar farashin man fetur da bayan gwamnatin tarayya ta cire tallafi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnatocin jihohin da ke gudanar da kamfanonin sufurin nasu na kansu, sun tabbatar da cewa farashin kudin mota zai ci gaba da zama kasa da na ‘yan kasuwa.
A Borno, Gwamna Babagana Zulum ya amince da sakin motocin bas guda 50 domin shawo kan lamarin tsadar sufuri a jihar, rahoton The Nation.
Cire Tallafi: Jihohi 3 A Arewacin Najeriya Sun Daukewa Dalibai Da Ma'aikata Wahalhalu, Sun Bayyana Tsarin
Yadda lamarin yake a jihar Borno
A cewar Mallam Isa Gusau, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, motocin bas din za a kara su ne a cikin jerin motocin sufuri mallakar Borno Express Corporation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gusau ya ce an kuma samar da motocin daukar kaya 30 domin bai wa manoma musamman wadanda ke zaune a cikin Maiduguri damar tafiya kyauta zuwa wajen birnin jihar inda gonakinsu suke.
Wani dalibin Jami’ar Maiduguri, Mustapha Abdullahi, da ma’aikacin gwamnati, Ali Modu wadanda ke morar amfani da motocin sun yaba da yunkurin.
A cewar Abdullahi:
"Ina hawa motocin bas din Borno Express a kullum, ina biyan N50 daga Post Office zuwa Jami'ar Maiduguri sabanin N150 da motocin haya da masu tuka keke napep ke karba.”
Yadda lamarin yake a jihar Adamawa
A Adamawa, gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti na musamman kan dakile radadin cire tallafin tare da nada Dokta Amos Edgar, shugaban ma’aikata na gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin shugaban kwamitin.
Edgar ya bayyana shirin gwamnatin Adamawa na siyan motocin bas na ma'aikata da kuma zirga-zirga tsakanin kananan hukumomi akan farashi mai sauki.
Ya ce sauran matakan da gwamnati ta dauka sun hada da amincewa da ba da tallafin Naira 10,000 ga duk ma’aikata da ‘yan fansho duk wata, The Paradise ta tattaro.
Mista Labaran Salisu, Daraktan Sufuri na Ma’aikatar Sufuri ta Adamawa, ya ce za a tura wasu daga cikin motoci 250 da aka yi hayarsu zuwa a ma’aikatar don ayyukan jahohi.
Yadda gwamnatin Yobe ta kawo dauki
A Yobe, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Dokta Mohammed Goje, ya ce ana shirin samar da hanyar sufuri kyauta ga dalibai da ma’aikatan gwamnati.
A cewar Goje:
"Nan kusa gwamnatin jihar za ta samar da motocin bas don sufuri kyauta ga ma'aikatan gwamnati da dalibai.”
Sai dai, a tattaunawar wakilin Legit Hausa da wani mazaunin jihar Yobe, Modu Hassan Abba, ya ce duk wani tallafi ana yinsa ne kan ma’aikatan gwamnati, ba tare da duba masu aikin zaman kansu ba.
A cewarsa:
“Muna biyan haraji, muna aiki don ci gaban kasa, amma ba a ta mu, sai a fara da ma’aikatan gwamnati, mu kam tsadar rayuwa ba ta kanmu ne?”
Asali: Legit.ng