Dakarun Soji Sun Kama Kasurgumin Ɗan Bindiga Da Wasu Hatsabibai 4 a Zamfara da Sokoto
- Gwarazan dakarun sojin Najeriya sun yi ram da wani babban ɗan ta'adda, Jabi Ruwa da hatsabiban yaransa hudu a Zamfara da Sokoto
- Wata majiya ta bayyana cewa sojojin sun samu wannan nasara ne bayan samun bayanan sirri ranar 28 ga watan Yuli, 2023
- A halin yanzu yan bindigan jejin da suka shiga hannu na karkashin bincike a hannun sojoji
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Dakarun sojin Operation Hadarin Daji (OPHD) da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Arewa maso Yamma sun cafke wani ƙasurgumin shugaban 'yan bindiga mai suna, Jabi Ruwa.
Haka nan kuma sojojin sun damƙe wasu kwamandojinsa hatsabibai guda 4 a wani samamen shara da suka kai jihar Zamfara da maƙociyarta jihar Sakkwato.
Wata babbar majiya a hukumar sojin Najeriya ta shaida wa jaridar Tribune ranar Asabar cewa baki ɗaya hatsabiban yan bindigan da aka kama suna ƙarƙashin bincike.
Jami'in sojan ya bayyana cewa rundunar Operation Hadarin Daji ta ƙara matsa ƙaimi a samamen da take kai wa maɓoyar ‘yan ta’adda a Arewa Maso Yamma.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, rundunar zata ci gaba da kai samame sansanonin yan bindiga da nufin kakkaɓe su a shiyyar Arewa maso Yamma wacce ta ƙunshi jihohin Kebbi, Katsina, Zamfara da Sakkwato.
Yadda yan ta'adda suka shiga hannun sojoji
Majiyar ta ce:
"A ranar 28 ga watan Yuli, 2023, muna samu wasu sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa wani ƙasurgumin ɗan bindigan daji mai suna Jabi Ruwa da yaransa huɗu sun ɓuya a ƙauyen Dambala."
"Bayan tattara bayanan ne dakarun sojin FOB da aka girke a Gwadabawa da sojojin da aka tura Raka, tare haɗin guiwar yan sa'kai suka haɗa tawaga suka durfafi ƙauyem Dambala, suka cafke su baki ɗaya."
Ganduje Ya Gamu da Cikas, Wasu Kusoshin APC Sun Faɗa Wa Tinubu Wanda Ya Cancanci Zama Shugaban APC Na Gaba
Majiyar ta bayyana cewa a halin yanzu Sojoji sun fara gudanar bincike amatakin farko kan dukkan mutanen da aka kama.
An Sako Bokan Da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Shi A Anambra
A wani rahoton na daban kuma Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta sanar da samun labarin sakin shahararren boka da 'yan bindiga suka yo garkuwa da shi.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar , DSP Tochukwu Ikenga shi ya bayyana sakin bokan a yau Asabar 26 ga watan Yuli a Awka, babban birnin Anambra.
Asali: Legit.ng