Yan Sanda Sun Bayyana Gaskiyar Yadda Wata Budurwa Ta Mutu a Otal a Anambra
- Rundunar 'yan sanda reshen jihar Anambra ta bayyana ainihin abinda ya yi ajalin wata budurwa a Otal ɗin Cosmila
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Tochukwu Ikenga, ya ce budurwar nutsewa ta yi ba duka ne ya yi ajalinta ba
- Da farko, an yaɗa labarin cewa mamaciyar ta kwashi kuɗi a wurin shagalin Bazday, matasa suka mata dukan kawo wuƙa har ta mutu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Anambra state - Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya, ta yi magana game da wata mata da aka tsinci gawar ta a wani wurin wanka a Otal din Cosmila da ke Awka, babban birnin jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Tochukwu Ikenga, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce rahoton binciken gawar da aka gudanar ya nuna cewa nutsewa ta yi a ruwa.
Ya ce labarin da ake yaɗa wa cewa dukanta aka yi har ta mutu ba gaskiya bane, binciken likitoci ya nuna cewa nutsewa ta yi a ruwa har rai ya yi halinsa, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
DSP Ikenga ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Saɓanin ikirarin da wasu suka yi cewa an yi wa budurwar dukan tsiya har ta mutu, likita ya gano babu alamun rauni a gawar matar."
Kakakin ‘yan sandan ya ce binciken ya yi daidai da rahoton farko na cewa budurwan ta gudu ne kan zargin sata a wurin taron, kuma ba a same ta ba bayan haka.
"Da alama ta fada cikin tafkin ruwan da ba a amfani da shi kuma ta nutse," in ji shi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Adeoye, ya umarci a mika takardar karar zuwa Ofishin Antoni Janar domin tantancewa da kuma ba da shawarwaarin shari’a.
Asalin labarin farko da ya yaɗu
Matar mai suna Chinyere Awuda, ‘yar shekara 27, an tsinci gawar ta ne a ranar 17 ga watan Yuli, a cikin wurin ninkaya na Otal, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
Misis Awuda, ‘yar asalin garin Nnobi a karamar hukumar Idemili ta kudu a Anambra, an zarge ta da ɗibar wasu kudade da ake watsawa mai bikin zagayowar ranar haihuwa a cin Otal ɗin.
An ce masu watsa kuɗin suka kamata kana suka yi mata duka har ta mutu, daga bisani kuma suka jefar da gawarta a wurin wanka. Lamarin da shugabannin wurin suka musanta.
DSS Ta Yi Rashin Nasara Kan Dakataccen Gwamnan CBN, Kotu Ta Yanke Hukunci
A wani labarin na daban Babbar Ƙotun Abuja mai zama a Maitama ta yi fatali da buƙatar hukumar DSS na ci gaba da tsare dakataccen gwamnan CBN.
A zaman ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, Alkalin Kotun ya yanke cewa babbar Kotu ba ta da hurumin sauraron bukatar.
Asali: Legit.ng