Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade 6 a Hukumar Kwastam Ta Kasa
- Shugaba Bola Tinubu ya yi sabbin naɗi guda 6 a hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) wata ɗaya da yan kwanaki bayan naɗa kwanturola janar
- Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Maiwada (CSC) ne ya bayyana sunayen waɗanda shugaban kasan ya naɗa
- Ya naɗa mataimakan kwanturola janar (DCG) guda uku da kuma ƙananan mataimakan kwanturola (ACG) guda 3
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa mataimakan kwanturola janar na hukumar kwastam guda 3 da kananan mataimaka guda 3.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa shugaba Tinubu ya amince da naɗin, F O Okun a matsayin mataimakin kwanturola janar (DCG) na hukumar kwastam ta ƙasa (NCS).
Sauran mutum biyu da shugaban ya naɗa a matsayin mataimakan kwanturola tare da Okun sun haɗa da, MBA Musa da kuma A Hamisu.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kwastam ta ƙasa, Abdullahi Maiwada (CSC), ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da sanyin safiyar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaba Tinubu ya amince da naɗa kananan mataimaka (ACG) guda uku
Haka zalika, shugaban ƙasar ya kuma naɗa sabbin kananan mataimakan kwanturo janar (ACG) guda 3, sun ƙunshi, K Olumoh, AB Mohammed da kuma A Alajogun.
Wannan naɗin na DCG da ACG na zuwa ne bayan shugaban ƙasa Tinubu ya naɗa sabon kwanturola janar a hukumar kwastam, Mista Bashir Adewale Adeniyi, ranar 19 ga watan Yuni, 2023.
A rahoton Sunnews, sanarwan ta ƙara da cewa:
"Kwanturola janar na hukumar, Bashir Adewale Adeniyi ya taya ɗaukacin waɗanda aka naɗa a matsayin mambobin gudanarwa murnar samun wannan matsayi."
"Ya buƙaci su tashi tsaye, su nunka ƙoƙarinsu domin tabbatar da ayyukan kwastam sun ƙara gaba musamman a bangaren nauyin da ke hanta na tara kudaɗen shiga, murkushe fasakwauri da saukaka kasuwanci."
Shugabancin APC: Bamu Yanke Waɗanda Zasu Cike Gurbi Ba, Felix Morka
A wani rahoton na daban Jam'iyyar APC ta ce har yanzu mahukunta ba su cimma mataaya kan wanda zai gaji kujerar Sanata Abdullahi Adamu ba.
Kakakin APC, Felix Morka, ya ce batun Ganduje da ake ta yaɗa wa duk jita-jita ce amma ba bu wata sanarwa a hukumance.
Asali: Legit.ng