Ahmed Musa Ya Ce Saboda Ragewa 'Yan Najeriya Radadi Ne Ya Sayar Da Fetur Kan N580 a Gidan Mansa
- Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan Ahmed Musa, ya bayyana dalilin da ya sanya shi sauke farashin man fetur a gidan mansa
- Ya ce ya lura da irin wahalhalun da 'yan Najeriya suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi
- Musa ya kuma sha alwashin bude karin wasu gidajen man kafin ya yi ritaya daga kwallon kafa
Kano - Shahararren dan wasan kwallon kafar nan Ahmed Musa, ya yi bayani kan dalilin da ya sa ya sauke farashin man fetur zuwa naira 580 a gidan mansa MYCA7 da ke Kano.
Musa ya ce ya yi hakan ne domin ragewa 'yan Najeriya radadin da cire tallafin man fetur ya jefa su a ciki kamar yadda The Punch.
Ya sanar da sauke farashin man fetur din ne daga naira 620 zuwa 580 ta shafinsa na Twitter ranar Litinin din da ta gabata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Yan Najeriya na cikin matsanancin hali
Tun ranar 29 ga watan Mayu da aka rantsar da shi, Shugaba Tinubu ya ce ba zai ci gaba da ba da tallafin man fetur ba.
Tun daga wancan lokacin ne akai ta samun hauhawar farashin man fetur din, inda yanzu haka ake sayar da shi kan naira 620 a wasu gidajen man.
Tashin farashin man ya janyo tsadar kudaden zirga-zirga da kuma tashin farashin kayayyakin amfani na yau da kullum.
Ahmed Musa ya ce yana da burin bude wasu gidajen man a Najeriya
A zantawarsa da jaridar The Punch a ranar Laraba, Musa ya ce ya yi hakan ne domin ragewa 'yan kasa wahalhalun da suke ciki.
Ya ce ya fahimci cewa mutane da dama na cikin mawuyacin hali wajen samun abinda za su jefa bakin salati.
Ya ce wannan ne wani dan abinda yake ganin zai iya yi wa mutanensa, kuma yana fatan bude karin wasu gidajen man a sassan Najeriya daban-daban kafin ya ajiye kwallo.
Cire tallafi: Gwamnonin Kwara da Ogun sun amince da bai wa ma'aikata tallafin N10,000
Legit.ng a baya ta yi rahoto da ke nuna cewa Dapo Abiodun na jihar Ogun, da Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara, sun amince da bai wa ma'aikatan jihohinsu naira 10,000 a matsayin tallafi.
Gwamnonin sun ce tallafin zai shafi har da dalibai da kuma 'yan fansho, ba wai ma'aikata kadai ba.
Asali: Legit.ng