Babbar Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar DSS Na Ci Gaba da Tsare Godwin Emefiele

Babbar Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar DSS Na Ci Gaba da Tsare Godwin Emefiele

  • Babbar Ƙotun Abuja mai zama a Maitama ta yi fatali da buƙatar hukumar DSS na ci gaba da tsare dakataccen gwamnan CBN
  • A zaman ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, Alkalin Kotun ya yanke cewa babbar Kotu ba ta da hurumin sauraron bukatar
  • Hukumar DSS ta ce ci gaba da tsare Emefiele ne bayan bankaɗo waso kwararan shaidu da suke buƙatar bincike

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Babbar Kotun birnin tarayya Abuja ta yi watsi da sabuwar buƙatar hukumar yan sandan farin kaya (DSS) na ci gaba da tsare dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Kotun ta yi watsi da buƙatar DSS wacce ta nemi ci gaba da tsare Emefiele na tsawon kwanaki 14, ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023.

Godwin Emefiele yayin da zai shiga Kotu a Legas.
Babbar Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar DSS Na Ci Gaba da Tsare Godwin Emefiele Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun mai shari'a Hamza Muazu, ya ce buƙatar da DSS ta shigar rashin mutunta tsarin shari'a ne kuma Kotun ba ta da hurumin sauraron ƙarar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Magantu Kan Rigimar Da Ta Faru Kan Emefiele a Kotu, Ta Faɗi Matakin Da Za Ta Ɗauka

Meyasa DSS ta buƙaci ci gaba da tsare Emefiele a hannunta?

Hukumar tsaron sirrin, a cikin takardar ƙarar da ta shigar mai lamba: FCT/HC/M/12105/2023, ta shaida wa kotun cewa ta bankado wasu sabbin shaidu da za su bukaci ta kara rike Mista Emefiele a hannun ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Don haka DSS ta roki kotun da ta ba ta damar ci gaba da tsare Emefiele na tsawon kwanaki 14, domin samun damar kammala binciken da take yi.

Yadda zaman Kotun ya gudana a Abuja

Yayin da aka kira karar, mai shari’a Muazu ya bukaci lauyan da ke wakiltar DSS, Victor Ejelonu ya yi bayani kan ko kotun na da hurumin amince wa da wannan bukata, duba da tanadin sashe na 293 da 296 na dokar gudanar da Shari'a.

Bayan lura da bayanan alkalin wanda ya tabbatar da cewa babbar kotun ba ta da hurumin bayar da umarnin, lauyan hukumar DSS, Mista Ejelonu, ya janye ƙarar nan take.

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Hukumar DSS Ta Sake Cafke Godwin Emefiele

Daga nan sai Alkalin, mai shari'a Mu'azu ya yi watsi da buƙatar DSS bisa hujjar cewa rashin mutunta tsarin tafiyar da shari'a ne, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Majalisar Dattawa Ta Amince da Nadin Mambobin Hukumar Raya Arewa Maso Gabas

A wani rahoton kuma Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin mambobin majalisar gudanarwa na hukumar raya yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Majalisar ta amince da naɗin mutanen bayan tantance su a zamanta na ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262