Cire Tallafi: Eniola Badmus Ta Goyi Bayan Tinubu, Ta Ce 'Yan Najeriya Na Shan Fetur Mafi Arha a Duniya
- Fitacciyar jarumar finafinan kudancin Najeriya Eniola Badmus, ta goyi bayan Tinubu kan cire tallafin man fetur
- Ta ce tana da tabbacin cewa shugaban yana da kyakkyawar manufa ga 'yan Najeriya
- Ta ce 'yan Najeriya da dama ba su da masaniya kan amfani cire tallafin man da gwamnatin ta Tinubu ta yi
Fitacciyar jarumar wasan kwaikwayo ta kudancin Najeriya Eniola Badmus, ta bayyana cikakken goyon bayanta ga shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Ta ce tana da yaƙinin cewa, Shugaba Tinubu yana da kyakkyawar manufa a zuciyarsa ga 'yan Najeriya.
Jarumar ta caccaki masu sukar Tinubu
Jarumar ta kuma caccaki mutanen da ke sukar Tinubu saboda cire tallafin man fetur da ya yi kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan za iya tunawa, jim kaɗan bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi, an samu tashin farashin man daga naira 190 zuwa 500 a duk lita.
Ana cikin hakan ne man fetur din ya yi tashin gwauron zabi zuwa naira 617 a duk lita, wanda hakan ya janyo korafe-korafe da dama daga 'yan Najeriya.
Da take zantawa da Daddy Freeze, shahararren mai amfani da kafar sada zumunta, Badmus ta ce har yanzu Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace arhar man fetur a duniya.
Masu sukar Tinubu ba su san amfanin cire tallafin man fetur ba
Ta bayyana cewa, da yawa daga mutanen da ke sukar Tinubu ba su da masaniya kan alfanun cire tallafin man fetur ɗin kamar yadda The Nation ta wallafa.
Ta ce tana da 'yancin faɗar ra'ayinta a matsayinta na 'yar ƙasa, kuma za ta iya goyon bayan duk wanda ta ga dama.
Ana Shirin Zanga-Zanga Yayin da TUC Ta Ba Tinubu Makonni 2 Don Kammala Tattaunawa a Kan Cire Tallafin Mai
Ta ce za ta ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu har zuwa lokacin da zai bar mulki saboda ta hango abubuwan alkhairin da zai yi wa 'yan kasa a gaba.
Tinubu ya yi ganawar sirri da ƙungiyoyin kwadago na ƙasa
Legit.ng ta yi rahoto a baya kan wata ganawar sirri da wakilan Shugaba Tinubu suka yi da wakilan kungiyar ƙwadago a fadar gwamnati.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadagon ta sha alwashin tsunduma yajin aiki muddun abubuwa ba su sauya ba.
Asali: Legit.ng