“Ba Zan Iya Yin Biyayya Ga Kowani ‘Da Namiji Ba”: Budurwa Ta Ce Burinta Shine Zama Uwa Ba Aure
- Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta bayyana a soshiyal midiya cewa burinta shine ta mallaki 'da ba tare da ta kasance a karkashin namiji ba
- Da take karfafa maganarta, matashiyar ta bayyana cewa ba za ta iya bin umurnin kowani 'da namiji ba
- Wannan furuci nata ya samu gagarumin goyon baya daga sauran yan mata wadanda suka yarda da ita, yayin da wasu kuma suka nuna rashin gamsuwa
Wata budurwa yar Najeriya, @thearabicgirl_skincare0, ta bayyana cewa ta so ta zama uwa ba tare da aure ba amma bata san yaya za ta sanar da mahaifiyarta ba.
A cewarta, ba za ta iya daukar umurni daga kowani 'da namiji ba kuma saboda haka bata tunanin yin aure.

Source: TikTok
Ta kara da cewar kasancewa mai dogaro da kanta da kuma jin dadin kudinta shine abun da ya fiye mata.

Kara karanta wannan
Budurwa Ta Dasa Kamarar CCTV a Gaban Kofarta, Ta Kama Makwabciya Da Ke Dauke Mata Kaya
"Ta yaya zan yi wa mahaifiyata bayani a shekaruna ina son zama uwa ba aure. Kawai ba zan iya yiwa kowani namiji biyayya bane. Ina da kudin," kalamanta a bidiyonta na TikTok.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yan mata da dama sun yarda da hujjarta, yayin da wasu suka ki amincewa da batun nata.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Sandypec ta ce:
"Ni ina son dukka biyu namijin kirki da kudi amma dai a matsayinki na mace ki yi kokari ki mallaki kudin kanki akwai dalili..."
vivianezike732 ta ce:
"Ki bata dukkan kudaden da wani gaye ya kamata ya bata ba za ta tuna cewa akwai aure ba."
Latioflagos ta ce:
"Ta yaya zan yi wa mahaifiyata bayani cewa bana son yin aure kuma bana son haihuwar 'ya'ya."
Onye ta ce:
"Na zata ni kawai ce ke son zama uwa ba aure shekaruna 19 amma bana tunanin ace na zama baiwar da namiji da sunan aure."
Chinonye Nwalie Ndia ta ce:
"Don Allah kada ki yarda wani ya matsa maki ki yi aure. Ina zaune lafiya cikin farin ciki a gidan aurena, kuma ina jin dadin biyayya ga mijina amma na san cewa aure ba na kowa bane."

Kara karanta wannan
“Na Fi Mijina Samun Kudi”: Matar Aure Ta Ce Bata Bude Asusun Hadin Gwiwa Ba a Gidan Aurenta
Ku harbe ni, ina son tafiya barzahu: Dan Najeriya ya kutsa kai sansanin sojin sama
A wani labari na daban, wani mutumi da ba a bayyana sunansa ba ya haddasa cece-kuce a sansanin sojoji yayin da ya bukaci sojoji da su bindige shi.
A bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, mutumin ya daga hannunsa na dama sama sannan ya dungi ihun 'Allah', cewa shi yana so a harbe shi don ya tafi barzahu.
Asali: Legit.ng