Babban Jigon Jam'iyyar PDP a Jihar Delta Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Delta ta yi babban rashin wani muhimmin jigonta a jihar
- Cif Charles Obude wanda ya taɓa yin takarar gwamna da Sanata a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar, ya mutu ne yana da shekara 65 a duniya
- Gwamnan jihar ya aike da saƙon ta'aziyyarsa kan mutuwar gogaggen ɗan siyasan wanda ya rasu bayan ya yi fama da jinya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Delta - Wani babban jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Delta, Cif Charles Obule, ya faɗi ya mutu a ƙaramar hukumar Sapele ta jihar.
Cif Charles Abule kafin mutuwarsa babban jigo ne na jam'iyyar kuma tsohon ɗan takarar gwamna da sanata a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Obule, wanda yake riƙe da sarautar “Erhi na masarautar Okpe” ya mutu ne a ranar Talata yana da shekara 65 a duniya bayan ya daɗe yana fama da rashin lafiya.
Gwamnan jihar Delta ya aike da saƙon ta'aziyyarsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin da ake ciki, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya nuna kaɗuwarsa kan mutuwar Obule wanda ya bayyana a matsayin sanannen jigo a jam'iyya, ɗan kasuwa, ɗan siyasa mai halin jin ƙai.
Gwamna Oborevwhori, a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sir Festus Ahon, ya fitar a ranar Laraba a birnin Asaba, ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga mutanen Sapele, masarautar Okpe da al'ummar ƙabilar Urhobo bisa mutuwar sanannen ɗan su.
A cewar gwamnan marigayin gogaggen ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa mai ayyukan jin ƙai wanda ya zama sananne a tsakanin mutanensa.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"A madadin gwamnatin jiha da al'ummar jihar Delta, ina miƙa saƙon ta'aziyyar gogaggen ɗan siyasa, Cif Charles Ufuoma Obule, wanda ya koma ga mahaliccinsa ranar Talata da yamma."
Babban Basarake Ya Rasu a Nasarawa
Rikicin APC: Tsohon Gwamna Zai Maye Gurbin Omisore a Kujerar Sakataren Jam'iyyar Na Kasa? Bayanai Sun Fito
A wani labarin kuma, an shiga jimamin babban rashin basarake mai daraja ta ɗaya a jihar Nasarawa, bayan ya koma ga mahaliccinsa.
Alhaji Aliyu Daudu basaraken Gadabuke a ƙaramar hukumar Toto ta jihar ya rasu ne yana da shekara 96 a duniya bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng