Majalisar Dattawa Ta Amince da Nadin Mambobin Hukumar Raya Arewa Maso Gabas

Majalisar Dattawa Ta Amince da Nadin Mambobin Hukumar Raya Arewa Maso Gabas

  • Majalisar dattawa ta amince da buƙatar shugaba Tinubu ta kafa majalisar gudanarwan hukumar raya Arewa maso Gabas
  • Sanatocin sun amince da naɗin ɗan ajinsu Muhammadu Buhari, Paul Tarfa a matsayin shugaban hukumar
  • Tun da fari, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya roƙi majalisar ta amince da naɗin mutane 10 a hukumar

FCT Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin mambobin majalisar gudanarwa na hukumar raya yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Ripples ta rahoto.

Waɗanda Sanatocin suka amince da naɗinsu sun haɗa da ɗan ajin su tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Janar Paul Tarfa daga Adamawa a matsayin shugaban hukumar.

Zauren majalisar dattijan Najeriya.
Majalisar Dattawa Ta Amince da Nadin Mambobin Hukumar Raya Arewa Maso Gabas Hoto: Senate
Asali: Facebook

Majalisar ta amince da naɗin mutanen bayan tantance su a zamanta na ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, 2023, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tun da fari, a wata wasiƙa da shugaban ƙasa ya aika kuma shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta, Tinubu ya nemi sanatoci su tantance tare da amince wa da naɗin mutanen.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Shugaban APC da Sakatare a Villa, Bayanai Sun Fito

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jerin mutanen da Tinubu ya naɗa kuma majalisa ta amince

Legit.ng Hausa ta tattaro muku sauran waɗanda majalisar ta amince da naɗinsu a hukumar raya shiyyar Arewa maso Gabas da muƙamansu, ga su kamar haka:

1. Musa Yashi - Daraktan sashin harkokin jin ƙai da walwala (Bauchi, Arewa maso Gabas)

2. Ahmed Abdulsalam Yahaya - Daraktan sashin ayyuka (Gombe, Arewa maso Gabas)

3. Dakta Abubakar Garba Ileah - Daraktan sashin gudanarwa da harkokin kuɗi (Yobe, Arewa maso Yamma)

4. Mohamed Goni Alkali - Manajan Darakta (Borno, Arewa maso Gabas)

5. Samuel Ifeanyi Onuigbo - Mamba (Abia, Kudu maso Gabas)

6. Honorabul Gambo Maikyau - Mamba ( Taraba, Arewa maso Gabas)

7. Abdullahi Abbas - Mamba (Kano, Arewa maso Yamma)

8. Zaf Steven Ondora - Mamba (Benue, Arewa ta Tsakiya)

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Hukumar DSS Ta Gurfanar da Dakataccen Gwamnan CBN a Kotu, Sabbin Bayanai Sun Fito

9. Chief Mutiu Lawal Areh - Mamba (Legas, Kudu maso Yamma)

10. Frank Achinike Owo - Mamba (Ribas, Kudu maso Kudu).

Shugaba Tinubu Ya Maida Martani Mai Zafi Kan Yunkurin Juyin Mulki a Ƙasar Nijar

A wani rahoton Shugaba Tinubu ya gargaɗi sojojin jamhuriyar Nijar, ya ce ECOWAS ba zata yarda da juyin mulki ba.

Rahotannin da suka fito daga Jamhuriyar Nijar da safiyar yau Laraba, 26 ga watan Yuli, 2023 sun nuna cewa an rufe fadar shugaban kasa da wasu ofisoshinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel