Yan Sandan Borno Sun Kama Mata 2 Da Wasu Mazaje 8 Bisa Zargin Halaka Jami'in Hukumar

Yan Sandan Borno Sun Kama Mata 2 Da Wasu Mazaje 8 Bisa Zargin Halaka Jami'in Hukumar

  • Yan sandan jihar Borno sun kama wasu mutane 10 bisa zargin kashe jami'in hukumar
  • Mutanen sun haɗa da maza 8 da kuma mata biyu waɗanda mafi yawancinsu matasa ne
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Yusuf ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Maiduguri jihar Borno - Jami'an ‘yan sandan jihar Borno, sun kama wasu mutane 10 da ake zargi da kashe wani ɗan sanda a Maiduguri babban birnin jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Yusufu, ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a gaban ‘yan jarida a hedikwatar rundunar a ranar Talata.

'Yan sandan Borno sun cafke mutane 10 bisa laifin halaka ɗan sanda
Rundunar 'yan sandan Borno ta kama mata 2 maza 8 bisa laifin halaka ɗan sanda. Hoto: Omar Yasiga
Asali: Facebook

Mutanen da ake zargi sun haɗa da maza 8 da mata 2

Mutanen da ake zargi da hannu a lamarin sun ƙunshi maza takwas da aka bayyana sunayensu da Usman Audu, ɗan shekara 20, Abba Bala, 20, Sunday Garba, 21, David Paul, 35, Mohammed Abubakar, 19, Jude Eze, 37, Amaechi Abdulsalam Afochibe, 37, da kuma Nduibuse Nnaji, mai shekaru 34.

Kara karanta wannan

Halin da Ake Ciki a Gidan Atiku Abubakar Bayan Kama 'Yan Ta'adda Suna Shirin Kai Hari, An Fara Ɗaukar Matakai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sannan an bayyana sunayen matan da aka kama tare mazan takwas da Hauwa Usman, mai shekaru 20 da kuma Aisha Musa mai shekaru 19 kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

An bayyana sunan ɗan sanda da aka kashe da Babagana Mala, wanda yake aiki a wani tsagi na 'yan sandan Malari da ke ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Yadda mummunan lamarin kisan ɗan sandan ya faru

Kwamishinan ya bayyana cewa ɗan sandan da aka kashe ya zo hutu ne gida wato Maiduguri a yayin da mummunan lamarin ya faru kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya ce an samu cacar baki tsakanin ɗan sanda da mutanen da suka kashe shi wanda a cikin hakan ne suka caka masa wani abu mai tsini da yi sanadin mutuwarsa.

Yusuf ya ƙara da cewar an sanar jami'ansu wanda suka zo cikin gaggawa sannan suka ɗauki jami'in zuwa asibiti, inda a can aka tabbatar da rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Emefiele: Jami'an DSS Sun Sake Cafke Dakataccen Gwamnan CBN, Sun Yi Awon Gaba da Shi Bayan Abinda Ya Faru

Ya kuma bayyana cewa wani ɗan gajeren bidiyo da wani ya ɗauka ne ya taimakawa jami'an 'yansa wajen kama mutanen da suka yi aika-aikar.

Sojoji sun halaka 'yan ta'adda shida a jihar Borno gami da ƙwato makamai da dama

A baya Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan 'yan ta'adda shida da sojoji suka yi nasarar halakawa a jihar Borno.

Sojojin sun kuma yi nasarar kama wani ɗan leƙen asirin 'yan ta'addan tare da ƙwato makamai masu tarin yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng