Rundunar Yan Sandan Kano Ta Ba Da Umurinin Gayyato Masu Tsokanar A.A. Rufa’i

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Ba Da Umurinin Gayyato Masu Tsokanar A.A. Rufa’i

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ƙuduri aniyar maganin masu tsokanar matashin nan A.A. Rufa'i
  • Rundunar ta ce za ta gayyaci duk masu tsokanarsa sakamakon umarnin da kwamishinan 'yan sandan jihar ya ba da
  • Hakan ya biyo bayan buƙatar da wasu lauyoyi da ke Kano suka shigar don ganin an takawa abin birki

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano, ta sanar da cewa za ta gayyaci masu tsokanar matashin mai taɓin ƙwaƙwalwa A.A. Rufa'i a kafafen sada zumunta.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

A cikin 'yan kwanakin nan ne dai ake yawan ganin guntayen bidiyoyi na Rufa'i a kafafen sada zumunta, inda yake yi wa mutane kyautar kuɗaɗen da suka wuce tunani.

Kara karanta wannan

Emefiele: Bidiyon Rikici Tsakanin Jami'an DSS Da Na Gidan Yari Kan Tafiya Da Tsohon Gwamnan Babban Banki Ya Bayyana

'Yan sanda jihar Kano za su gayyaci masu tsokanar A.A. Rufa'i
'Yan sanda Kano sun ce za su gayyaci mutanen da ke tsokanar A.A. Rufa'i. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya ba da umarnin gayyato masu tsokanar Rufa'i

Sanarwar ta Kiyawa ta bayyana cewa kwamshinan 'yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel ne ya bayar da umarnin gayyatar masu tsokanar A.A. Rufa'i zuwa ofishin hukumar.

Kiyawa ya ƙara da cewa hakan ya biyo bayan koke da wata ƙungiya ta lauyoyi ta shigar don ganin ta kawo ƙarshen cin zarafin da mutane ke yi ma sa.

A kalamansa:

“Lauyoyi sun shigar da ƙorafi akan masu amfani da rashin lafiyar matashin da akewa laƙabi da Alhaji AA Rufa'i. Yanzu haka, Mai Girma Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, psc ya bada umarnin a faɗaɗa bincike tare da gayyato wasu daga cikin mutanen da ake zargi da amfani da lalurar sa wajen tunzura shi.”

'Yan uwansa sun gargaɗi mutane kan tsokanarsa, za su ɗauki mataki na shari'a

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: Jami'ar Najeriya Za Ta Gwangwaje Ma'aikata Da Dalibanta Da Kayan Tallafi

Wani daga cikin makusantan A.A. Rufa'i a kwanakin baya ya bayyana cewa ba sa jin daɗin abinda jama'a ke yi ma sa duba da cewa lalura ce ta same shi ba cikin hayyacinsa yake abubuwan da yake yi ba.

A cikin hirarsa da aka wallafa a shafin rediyon Freedom, ɗan uwan Rufa'i mai suna Bashir Muhammad Sani ya bayyana cewa suna matuƙar jin takaicin abinda jama'a ke yi masa.

Ya ce shi ba ɗan wasan kwaikwayo ba ne amma duk mutane sun bi sun takura ma sa da tsokana ba tare da la'akari da halin taɓin hankali da ya tsinci kansa a ciki ba.

A dalilin hakan ne Bashir ya gargaɗi duk masu tsokanarsa da su daina, domin kuwa sun shigo da hukuma cikin lamarin, kuma za ta hukunta duk wanda aka samu yana tsokanarsa.

'Yan sanda sun gano motar da aka sata daga Nasarawa a jihar Taraba, sun kama mutane 2

A wani rahoto da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa jami'an 'yan sandan jihar Nasarawa, sun yi nasarar gano wata mota da aka sace daga jihar sannan aka tafi da ita jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Hayakin Janareto Ya Yi Sanadin Rasuwar Ma'aurata, 'Yayansu Da Mutane 2 a Anambra

Haka nan kuma jami'an 'yan sandan, sun yi nasarar cafke mutane biyu da suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng