NLC: Kungiyar Kwadugo Ta Sanar da Tsunduma Yajin Aiki Daga Watan Agusta
- Kungiyar kwadugo ta bayyana cewa zata tsunduma yajin aikin gama gari daga ranar 2 ga watan Agusta, 2023
- NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin mako guda ta sauya tare-tsaren da ta bullo da su na yaƙi da talakawa
- A cewar NLC, matuƙar gwamnatin shugaba Tinubu ba ta canja tsare-tsaren ba, zata haɗa 'ya'yanta su fara yajin aikin sai baba ta gani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 7 ta sake nazari kan tsare-tsarenta da suka haddasa tsadar rayuwa a Najeriya.
Vanguard ta rahoto cewa NLC ta buƙaci FG ta janye waɗan nan tsare-tsare da suka jefa talakawa cikin halin ƙaƙanikayi, ciki harda tashin farashin litar man fetur na kwanan nan.
Ƙungiyar ta bai wa gwamnati mako ɗaya ta sauya waɗannan tsare-tsaren na yaƙi da talakawa ko kuma a fuskanci yajin aikin gama gari daga ranar 2 ga watan Agusta, 2023.
Emefiele: Bidiyon Rikici Tsakanin Jami'an DSS Da Na Gidan Yari Kan Tafiya Da Tsohon Gwamnan Babban Banki Ya Bayyana
NLC ta aike da saƙo da kawayenta da rassan jihohi
Bisa haka, ƙungiyar NLC ta yi kira ga sauran ƙawayenta kungiyoyin ma'aikata da sauran 'yan Najeriya fararen hula, da rassan ƙungiyar na jihohi su fara shiri tun yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta umarci rassan NLC na jihohi su fara harhaɗa kan ma'aikata domin fara yajin aikin gama gari da kuma gagarumar zanga-zanga a faɗin Najeriya idan har FG ta gaza biyan buƙatunta.
Jaridar Tribune ta tattaro cewa wannan na ɗaya daga cikin matakan da NLC ta cimma matsaya a wurin taron kwamitin gudanarwan ƙungiyar (CWC) ranar Talata, 25 ga watan Yuli.
Wannan taro na kwamitin CWC na NLC ta ƙasa ya gudana ne a hedkwatar ƙungiyar 'Labour House' a babban birnin tarayya Abuja.
Rayuwa ta ƙara taada a Najeriya tun bayan cire tallafin man fetur da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi. Kwatsam kuma aka ƙara farashin litar mai wanda ya haura N600 a yanzu.
Rashin Biyan Kudin Shagulgula Ya Sanya Amarya Ta Soke Aurenta Ana Saura Sati 1 Biki, Iyaye Sun Ba Ta Muhimmiyar Shawara
Dele Farotimi: Shugaba Tinubu Ba Zai Nada Ministocin da Zasu Gyara Najeriya Ba
Kuna da labarin Wani ɗan gwagwarmaya kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Dele Farotimi, ya ce Tinubu ba zai naɗa mutanen kirki a matsayin ministoci ba.
Farotimi ya ce ‘ya’yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ba su da kishin kasar nan a zuciyoyinsu.
Asali: Legit.ng