Hukumar DSS Ta Sake Cafke Emefiele Ne Bisa Zargin Daukar Nauyin Ta'addanci

Hukumar DSS Ta Sake Cafke Emefiele Ne Bisa Zargin Daukar Nauyin Ta'addanci

  • Duk da babbar kotun tarayya ta bayar da belin Godwin Emefiele, jami'an hukumar DSS sun sake cafƙe shi a harabar kotu
  • Hukumar DSS dai har yanzu ba ta ce komai ba dangane da dalilin da ya sanya ta sake dakataccen gwamnan na CBN
  • Sai dai, wani majiya mai tushe ya bayyana laifukan da ake tuhumar Emefiele da su da suka sanya jami'an na DSS suka sake cafke shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ikoyi, Legas - Jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun sake cafke dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, a ranar Talata bayan kotu ta bayar da belinsa kan N20m.

Sake cafke dakataccen gwamnan ya auku ne bayan jami'an DSS da na hukumar gidajen yarin Najeriya sun ba hammata iska kan tafiya da Emefiele, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Godwin Emefiele: Abubuwa 5 Da Yakamata Ku Sani Yayin Da DSS Ta Sake Cafke Dakataccen Gwamnan CBN a Kotu

Dalilin da ya sanya DSS ta sake cafke Emefiele
Zargin daukar nauyin ta'addanci ya sanya DSS ta sake cafke Emefiele Hoto: @NTANewsNow
Asali: Twitter

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, hukumar DSS ba ta fitar da sanarwa ba domin bayyana dalilin da ya sanya ta sake cafke dakataccen gwamnan na CBN. 

Amma wani majiya kan lamarin ya gayawa jaridar Daily Trust cewa an sake cafke Emefiele ne bisa umarnin kamu da aka samo daga wajen wata kotun majistare.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyar ya bayyana cewa an samu umarnin cafke Emefiele ne bisa zarginsa da ɗaukar nauyin ta'addanci.

A kalamansa:

"Umarnin kamun dai an samo shi ne bisa zargin ɗaukar nauyin ta'addanci. Ba mu san haƙiƙanin abinda umarnin kamun ya kunsa ba saboda lauyoyin dake kare shi ba su samu kwafi ba."
"Ba mu san dalilin da ya sanya DSS za ta samo umarnin kamu daga wajen kotun majistare ba bayan babbar kotun tarayya ta bayar da belinsa. Wannan tsantsagwaron kama karya ne."

Kara karanta wannan

Emefiele: Jami'an DSS Sun Sake Cafke Dakataccen Gwamnan CBN, Sun Yi Awon Gaba da Shi Bayan Abinda Ya Faru

DSS ba ta ce komai ba

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya ci tura domin ba a same shi a waya ba.

Lokacin da aka tura masa saƙo ta WhatsApp domin ya bayyana daliliin da ya sanya aka sake cafke dakataccen gwamnan na CBN, Afunanya ya ƙi ya ce komai dangane da lamarin.

Sannan kuma bai dawo da saƙonnin da aka tura masa ta waya ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

DSS Sun Sake Cafke Emefiele Duk Da Umarnin Kotu

Rahoto ya zo cewa jami'an hukumar DSS sun sake yin awon gaba da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele duk da umarnin kotu..

Babbar kotun tarayya dai ta bayar da belin Emefiele kan N20m, amma jami'an hukumar ta DSS sun sake cafke shi bayan sun ba hammata iska tsakaninsu da jami'an hukumar gidajen yarin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng