'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji Bakwai a Wani Hari a Jihar Zamfara

'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji Bakwai a Wani Hari a Jihar Zamfara

  • Ƴan bindiga sun halaka sojoji bakwai a wani mummunan kwanton ɓauna da suka yi musu a wani ƙauye a jihar Zamfara
  • Dakarun sojojin suna kan hanyar kai agajin gaggawa ne bayan ƴan bindigan sun farmaki wani ƙauye, lokacin da aka yi musu kwanton ɓauna
  • A lokacin harin ƴan bindigan sun halaka aƙalla mutum 20 a ƙauyen da suka kai farmaki cikin ƙaramar hukumar Maru

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun halaka jami'an sojoji mutum bakwai a wani kwanton ɓauna da suka yi musu a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Kangon Garacce a yankin Dangulbi, cikin ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, ranar Litinin inda suka halaka mutane da dama.

Yan bindiga sun halaka sojoji bakwai a Zamfara
'Yan bindigan sun yi wa jami'an tsaron kwanton bauna ne Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Wani mazaumin Dangulbi mai suna, Lawal Dangulbi, ya gayawa Channels tv a ranar Talata cewa sojojin sun je kai ɗauki ne a ƙauyen bayan sun samu kiran gaggawa kan harin da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen, lokacin da aka yi musu kwanton ɓauna.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Arewacin Najeriya, Sun Sace Bayin Allah Da Kona Motocin Jami'an Tsaro

"Ƴan bindigan sun raba kansu ne, wasu suna kai hari a ƙauyen yayin da wasu suka tsaya a wajen ƙauyen domin hana sojoji kai wa mutanen ƙauyen ɗauki, sun yi wa sojojin kwanton ɓauna inda suka halaka bakwai daga cikinsu." A cewarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ƴan bindigan sun kuma halaka mutane masu yawa a yayin harin

A cewarsa aƙalla mutum 20 mazaunan ƙauyen ƴan bindigan suka halaka a yayin harin, a cewar rahoton Ripples Nigeria.

Duk da dai har yanzu hukumomin sojoji a jihar Zamfara basu ce komai ba dangane da lamarin, wani majiya daga ɓangaren sojoji wanda ya san halin da ake ciki dangane da lamarin, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya bayyana cewa jami'an sojoji bakwai aka halaka a mummunan harin na ranar Litinin.

Ƴan bindiga sun daɗe suna kai farmaki a jihar Zamfara inda suka halaka mutane da dama da lalata dukiyoyi, yayin da a wasu lokutan su ke sace mutane domin biyan kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Mutane Sama da 100 Kan Zargin Aika Muggan Laifuka Daban-Daban a Arewa

Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga a Zamfara

A wani labarin kuma, dakarun sojoji sun samu nasarar daƙile harin ƴan bindiga lokacin da suka yi yunƙurin farmakar sansanin sojoji a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin na atisayen 'Operation Hadarin Daji' a yayin daƙile harin sun sheƙe miyagun ƴan bindiga bakwai tare da raunata wasu masu yawa daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng