Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban Kwalejin Ilmi a Jihar Ogun

Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban Kwalejin Ilmi a Jihar Ogun

  • Ƴan bindiga sun sace tsohon shugaban kwalejin ilmi ta gwamntin tarayya dake Osile, Abeokuta a jihar Ogun
  • Ƴan bindigan sun sace Dr Ayodele Ajayi Adele ne tare da matarsa da direbansa akan titin hanyar Abeokuta-Ibadan
  • Jami'an tsaro sun bi bayan ƴan bindigan domin kuɓuto da Dr Ajayi da sauran mutanen da suka kaɗa cikin daji

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace tsohon shugaban kwalejin ilmi ta gwamnatin tarayya dake Osile, Abeokuta jihar Ogun, Dr. Ayodele Ajayi ranar Talata.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa an sace Ajayi ne tare da matarsa da direbansa da misalin ƙarfe 7:17 na dare a ƙauyen Ikija, na ɓangaren Olodo kan titin hanyar Abeokuta-Ibadan a ƙaramar hukumar Odeda ta jihar Ogun.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Arewacin Najeriya, Sun Sace Bayin Allah Da Kona Motocin Jami'an Tsaro

'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban kwalejin ilmi
Yan bindiga sun sace Ajayi ne tare da matarsa da direbansa Hoto: Fceabk.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun sako matar Ajayi daga baya yayin da suka yi awon gaba da shi da direbansa.

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi da a sakaya sunansa ya bayyana cewa ƴan bindigan sun fito ne daga cikin daji inda suka farmaki Ajayi tare da sauran masu motoci akan hanyar, rahoton Channels tv ya tabbatar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewa ƴan bindigan waɗanda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi, sun tare hanyar ne sannan suka yi awon gaba da mutanen.

Majiyar wanda ya koka kan yadda yawaitar satar mutane ta ƙaru a yankin na Olodo kan titin hanyar Abeokuta-Ibadan, ya yi zargin cewa aƙalla mutum biyar aka sace a yankin cikin mako guda.

"Duka jiya fa ƴan bindiga suka sace mutum biyar, amma an sako biyu daga cikinsu daga baya." A cewarsa.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

"Haka kuma, watan da ya gabata an halaka mutum uku. Daga cikinsu akwai wani sanannen ɗan kasuwa mai wata babbar gona a yankin."

Ƴan sanda sun tabbatar da sace Dr Ajayi

Da aka tuntuɓesa kan lamarin, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Omolola Odutola ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ƙara da cewa ƴan sanda da sauran jami'an tsaro sun bi bayan ƴan bindigan domin cafko su.

'Yan Bindiga Sun Sace Mutane a Jihar Neja

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun kai farmaki wani ƙauye a jihar Neja, inda suka sace mutum uku da ɓarnata dukiya mai yawa.

Ƴan bindigan sun kuma ƙona wasu gidaje da raunata jami'an ƴan sanda biyu a yayin farmakin da suka kai ƙauyen Garin Gabas na ƙaramar hukumar Rafi ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng