Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Shari'ar Ganduje Ta Bidiyon Dala
- Babbar kotun tarayya mai sauraron ƙarar tsohon gwamnan jihar Kano kan hana hukumar PCACC cafke shi ta sanya ranar yanke hukunci
- Kotun ta sanya ranar 22 ga watan Satumba domin yin hukunci kan ƙarar Ganduje na neman ta hana hukumar PCACC kama shi
- Hukumar PCACC dai ta gayyaci tsohon gwamnan zuwa gabanta domin amsa tambayoyi kan bidiyonsa yana cusa dala a aljihu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin Kano ta sanya ranar 22 ga watan Satumba domin zartar da hukunci kan ƙarar Ganduje na neman a dakatar da shirin cafke shi kan bidiyon dala.
A ranar a 7 ga watan Yuli, kotu ta hana hukumar karɓar koke-koke da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jihar (PCACC) da ƴan sanda da wasu mutum shida daga gayyata ko cafke Ganduje, yalansa ko kuma waɗanda suka yi aiki a ƙarƙashinsa.
Ganduje ya buƙaci kotun da ta ba da umarnin hana hukumar PCACC bincikensa ko gayyatarsa kan bidiyon dala da ake zarginsa da shi.
Daily Trust tace a zaman da aka ci gaba ranar Talata, lauyan Ganduje, Matthew Burkaa (SAN) ya ce ƙarar an shigar da ita ne domin kare haƙƙin Ganduje sannan ya nemi ya kare iyalansa da masu riƙe da mukaman siyasa a gwamnatinsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Mai girma mai shari'a ba muna cewa kada a gayyaci Ganduje ko a bincike shi ba ne, aa sai dai a bi tsarin da doka ta gindaya." A cewarsa.
Sai dai lauyan PCACC, Femi Falana (SAN), ya gayawa kotun cewa kariyar da Ganduje yake da ita ta ƙare a ranar 29 ga watan Mayu bayan wa'adin mulkinsa ya ƙare.
"Wannan shari'ar ta danganci buƙatun jama’a ne ba abu ne na bukatar kai da kai ba. Mai shigar da ƙara na son a yi amfani da doka domin kare mutuncinsa da kuma kare ɓangarorin da ba sa a gaban kotu." A cewarsa.
Emefiele: Bidiyon Rikici Tsakanin Jami'an DSS Da Na Gidan Yari Kan Tafiya Da Tsohon Gwamnan Babban Banki Ya Bayyana
Femi Falana ya bayyana cewa kotu ba za ta iya kare wadanda basu bayyana a gabanta ba.
Lauyan PCACC ya buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar da Ganduje ya shigar
Babban lauyan ya kuma buƙaci kotun da ta yi watsi da buƙatar wanda ya shigar da ƙara, rahoton Aminiya ya tabbatar.
Lauyan rundunar ƴan sanda, Sunday Ekwe da na hukumar DSS, I B Bulus, sun amince da matsayar hukumar PCACC.
Lauyan Antoni Janar na jihar Kano, Khalifa Hashim, ya shigar da buƙatu uku a gaban kotun inda ya nemi kotun da ta yi watsi da ƙarar.
Bayan ya gama sauraron dukkanin ɓangarorin, mai shari'a A. M Liman, ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 22 ga watan Satumba domin yanke hukunci.
Gwamnatin Jigawa Na Son Kwsto Kadarorinta a Wajen Gwamnatin Kano
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Jigawa na neman a ƙwato mata wasu muhimman kadarorinta daga wajen gwamnatin jihar Kano.
Gwamnatin jihar ta nemi hukumar PCACC ta jihar Kano da ta ƙwato mata kadarorinta waɗanda aka cinye a jihar Kano.
Asali: Legit.ng