Abubuwa 5 Da Yakamata Ku Sani Yayin Da DSS Ta Sake Cafke Emefiele a Kotu
Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, an bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Ikoyi har sai ya cika sharuɗɗan belinsa, amma jami'an rundunar ƴan sandan farin kaya sun sake cafke shi a harabar kotun.
Premium Times ta rahoto cewa sharuɗɗan neman belin Emefiele sun haɗa da biyan tsabar kuɗi har N20m.
Ga abubuwa biyar da yakamata ku sani dangane da tsare Emefiele
Laifukan Emefiele na bayar da beli ne
Mai shari'a Nicholas Oweibo na babbar kotun tarayya a Ikoyi jihar Legas, ya yanke hukunci cewa laifukan Emefiele za a iya bayar da beli a kansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Emefiele, ta hannun lauyansa, Joseph Daodu, ya shigar da neman beli a gaban kotun inda ya musanta tuhumomi biyu da ake masa na mallakar bindiga da harsashi ba bisa ƙa'ida ba.
Emefiele: Jami'an DSS Sun Sake Cafke Dakataccen Gwamnan CBN, Sun Yi Awon Gaba da Shi Bayan Abinda Ya Faru
Emefiele ya buƙaci kotu ta bada belinsa bisa sanin da aka yi masa
Daodu ya gayawa kotun cewa yakamata a bayar da belin Emefiele bisa sanayya har sai kotun ta kammala sauraron ƙarar domin yanke hukuncinta.
Emefiele ya ƙi ya ba DSS fasfo ɗinsa
Nkiru Jones-Nebo, mataimakin darektan tuhuma a ofishin Antoni Janar na tarayya, ya gayawa kotun ta yi fatali da neman belin Emefiele, inda ya ce ba a ba gwamnatin tarayya isashshen lokacin da za ta yi martani ba.
Jones-Nebo ya gayawa kotun cewa suna da bayanin cewa Emefiele ya ƙi ya bayar da fasfo ɗinsa, wanda hakan na nuni da cewa dakataccen gwamnan na CBN zai iya guduwa daga shari'ar da ake masa.
Jami'an DSS da NCS sun ba hammata iska kan tafiya da Emefiele
Jami'an DSS da na hukumar gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCS) sun ba hammata iska a harabar kotu bayan an bayar da belin Emefiele.
Emefiele: Bidiyon Rikici Tsakanin Jami'an DSS Da Na Gidan Yari Kan Tafiya Da Tsohon Gwamnan Babban Banki Ya Bayyana
Sai dai, abinda doka ta tanada ya nuna kamata ya yi Emefiele ya ci gaba da kasancewa a hannun NCS bayan kotu ta bayar da belinsa.
Dambarwar dake cikin cafke Emefiele
An cafke Emefiele ne bayan Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa. Emefiele ya shirya neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, inda har hotuna da motocinsa aka fara rabawa.
Ƙin fitowa ya musanta cewa ba takara zai yi ba, shi ne abinda ya ƙara jefa shi cikin matsala. Dakataccen gwamnan CBN ɗin kuma ya riƙa aiwatar da wasu abubuwa da suka ci karo da aikin ofishinsa.
Jami'an DSS Sun Sake Cafke Emefiele
Rahoto ya zo cewa jami'an rundunar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun sake cafke dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Jami'an na DSS sun sake cafke Emefiele ne a harabar kotu duk da cewa kotun ta bayar da belinsa kan kudi N20m.
Asali: Legit.ng