Tafiya Da Emefiele Ta Sa An Samu Hatsaniya Tsakanin Jami'an DSS Da Na Gidan Yari

Tafiya Da Emefiele Ta Sa An Samu Hatsaniya Tsakanin Jami'an DSS Da Na Gidan Yari

  • A yayin da lauyoyin Emefiele ke ƙoƙarin cika sharuɗan belinsa, rikici ya ɓarke tsakanin jami’an DSS da jami’an NCS, waɗanda dukkansu ke ƙoƙarin ajiye shi a hannunsu
  • Ma’aikatar shari’a ta tarayya ce ta gurfanar da Emefiele a gaban kuliya bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba sai dai an ba da belinsa kan kuɗi naira miliyan 20
  • An yi fargabar cewa jami'an na DSS na shirin sake kama tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), duk da belin da ya samu

Legas - An samu wata 'yar hatsaniya a babbar kotun tarayya da ke Legas, tsakanin jami’an tsaro na farin kaya DSS da kuma jami'an Hukumar gidajen gyaran hali ta Najeriya(NCS).

An yi takun sakar ne kan wanda ya kamata ya ci gaba da ajiye tsohon gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele a wurinsu kamar yadda Channels TV ta wallafa a wani dan gajeren bidiyo.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotu Ta Bada Belin Dakataccen Gwamnan CBN Emefiele Kan N20m da Wasu Sharuɗda

An yi rikici tsakanin jami'an DSS da na NCS a Legas
An samu rikici tsakanin jami'an DSS da na NCS kan tafiya da Emefiele a Legas. Hoto: @thecableindex
Asali: Twitter

Ana tuhumar Emefiele da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba

Ma’aikatar shari’a ta tarayya ce ta gurfanar da Emefiele a gaban kuliya, bisa zargin mallakar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai an bayar da belinsa a kan kudi naira miliyan 20 tare da sharaɗin kawo wani mutum daya da zai tsaya masa, biyo bayan musanta zargin da kuma neman a wankesa da ya yi kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Haka nan kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare Godwin Emefiele a hannun jami'an hukumar gidajen gyaran hali (NCS), har zuwa lokacin da sharuɗan Berlin nasa za su kammala.

Yadda faɗa ya ɓarke tsakanin DSS da jami'an NCS kan Emefiele

Jim kaɗan bayan yanke hukunci, jami'an DSS sun matso da motarsu bakin kotun domin tafiya da Emefiele saɓanin umarnin da kotun ta ba da na ajiye shi a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Bidiyon Rashin Da’a Ga Musulunci: MURIC Ta Caccaki Davido, Ta Bukaci DSS Da Ta Gayyaci Mawakin

Hakan ne ya sa babban lauyan Emefiele da sauran lauyoyinsa bayyana fargabar cewa DSS na shirin sake kama wanda suke karewa.

Sai dai ana cikin tada jijiyoyin wuyan ne aka ga jami'an na hukumar gidajen gyaran halin sun ƙyale jami'an DSS sun tafi da Emefiele a motarsu domin gudun zubar da jini.

Kalli bidiyon a kasa:

An cire sunayen Wike, Ganduje da Bagudu daga ministocin Tinubu

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa an cire sunayen tsofaffin gwamnoni uku wato Wike, Ganduje da kuma Bagudu daga jerin waɗanda zai bai wa ministoci.

Wata mamba a jam'iyyar APC mai suna Sa'adatu Maccido ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng