Kotu Ta Bada Belin Dakataccen Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Babbar kotun tarayya mai zama a Ikoyi, jihar Legas ta bada belin dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele kan kuɗi N20m
- Alkalin Kotun mai shari'a Nicolas Oweibo ya gindaya sharuɗɗa masu tsauri kafin sakin Emefiele a matsayin beli
- A ɗazu ne jami'an DSS suka gurfanar da tsohon gwamnan CBN a gaban Kotu bisa zargin mallakar makamai ba kan doka ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Lagos State - Ƙotu ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, kan kudi naira miliyan 20.
Sharuɗɗan da Kotun ta gindaya na belin sun haɗa da gabatar da wanda zai tsaya masa, wanda ya mallaki kadarori a kewayen inda Kotu ke zama a Ikoyi, jihar Legas.
Haka zalila shi kansa, Emefiele, zai miƙa Fasfonsa na tafiye-tafiye sannan kuma ya gabatar da ma'aikacin gwamnatin da zai tsaya masa, wanda bai gaza mataki na 16 ba.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Emefiele ya jima a tsare kafin daga bisani aka gurfanar da shi gaban mai shari'a Nicholas Oweibo na babbar kotun tarayya da ke Legas, ranar Talata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane zarge-zarge gwamnatin tarayya ke wa Emefiele?
Masu shigar da kara suna tuhumar Mista Emefiele da mallakar bindiga ƙirar JOJEFF MAGNUM 8371 ta haramtacciyar hanya watau mara lasisi.
Jami'an hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS) ne suka kawo tsohon gwamnan CBN ɗin gaban Kotu cikin tsattsauran tsaro ranar Talata, 25 ga watan Yuli, 2023.
Vanguard ta rahoto cewa Jami'an DSS tare da Emefiele sun isa harabar Kotu da misalin ƙarfe 9:23 na safiyar Talata a cikin motar Hillux fara, wacce aka rufe lambarta.
Daga isarsu Kotun, Mista Emefiele ya fito daga motar tare da taimakon wata mata wacce har kawo yanzu ba a iya tantance bayananta ba.
Bayan haka ne kuma aka gurfanar da shi gaban Kotun karkashin mai shari'a Nicolas Oweibo, wanda zai jagoranci shari'ar.
Gwamna Uba Sani Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci a Kaduna
A wani labarin kuma Gwamna Malam Uba Sani na jihar Kaduna ya yi sabbin naɗe-naɗe masu muhimmanci a gwamnatinsa.
Uba Sani ya bayyana cewa ya yi la'akari da tarihin siyasa, gaskiya da riƙon amana da sadaukarwa wajen gina jihar Kaduna yayin zaƙulo mutanen da ya naɗa muƙaman.
Asali: Legit.ng