Tagwaye Da Suka Auri Yan Tagwaye a Rana Daya Sun Haifi Yan Bibbiyu

Tagwaye Da Suka Auri Yan Tagwaye a Rana Daya Sun Haifi Yan Bibbiyu

  • Wani bidiyo ya sake bayyana a soshiyal midiya wanda ke nuna yara hudu da wasu yan biyu suka haifa
  • Tagwayen matan wadanda suka haifi yan bibbiyu sun aure wasu tagwaye masu suna Sa'ad da Sa'eed Yusuf
  • Abun mamaki shine tagwayen, Sa'ad da Sa'eed Yusuf sun auri tagwayen matan a rana daya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani hoto da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno wasu jarirai hudu da wasu tagwayen mata biyu suka haifa.

Tagwayen matan ne suka haifi yaran hudu a matsayin yan bibbiyu yan awanni a tsakani, kuma sun yi aure ne a rana guda.

Allah ya azurta yan biyu da haihuwar yan bibbiyu
Tagwaye Da Suka Auri Yan Tagwaye a Rana Daya Sun Haifi Yan Bibbiyu Hoto: TheCable Lifestyle.
Asali: UGC

Iyayen yaran maza ma tagwaye ne

Wani abun da zai kara ba mutane sha'awa shine cewa iyayen yaran maza ma tagwaye ne kuma tare aka haife su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

Sunan mahaifan yaran Sa'ad da Sa'ed Yusuf, kuma sun auri tagwayen, wadanda suka haifa masu yaran a rana daya.

An dauki hotunan Sa'ad da Sa'eed tare da yaransu.

An haifi yaran a ranaku daban-daban, awanni 48 a tsakani

Rahotannin da ke yawo a soshiyal midiya ya ce sun haihu a kwanan nan kuma cewa a rana daya ne, sai dai a wata hira da TheCable Lifestyle, daya daga cikin mahaifan yaran maza ya ce tun a 2015 ne sannan cewa an haifi yaran ne a ranaku daban-daban.

Yayin da matar Sa'ad ta haifi tagwaye mata a ranar 15 ga watan Yuni, matar Sa'eed ta haifi yan maza biyu a ranar 17 ga watan Yuni. Su dukka sun haifi yaran ne ta hanyar tiyata.

Sa'ad ya ce:

"Ina mamakin dalilin da yasa mutane suka sauya labarin ba tare da sun tuntubi mutanen da abun ya shafa ba. Abun shine cewa mu tagwaye ne, kuma buka haifi tagwaye. Kuma dukkanmu muna auren tagwaye ne. Rahotannin cewa an haifesu a rana daya ba daidai bane.

Kara karanta wannan

A Kurarren Lokaci, Tinubu Ya Cire Mutum 4 a Jerin Wadanda Za A Ba Kujerar Minista

"Ko mu mun son da ma a rana daya aka haife su, ba za mu iya canja abun da Allah ya kaddara irin wannan ba. Ba mu iya yin wannan ba.Saboda dukkan iyayen akwai aka yi masu.
"Akwai tazarar kwanaki biyu a tsakanin tagwayen biyu. Lokacin da mutane suka yi magana kan haka a soshiyal midiya, sai suka sa abun ya yi kamar jiya-jiya ya faru."

Bidiyon amarya tana nunawa angonta kauna a wajen budar kansu ya dauka hankali

A wani labarin, an dauki bidiyon wani yanayi mai kayatar da zukata tsakanin wata amarya da angonta a wajen shagalin bikinsu sannan aka yada shi a TikTok, inda daga nan kuma ya yadu.

Bidiyon ya nuno angon yana cire mayafin da ya lullube fuskar amaryar a hankali a yayin budar kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng