Daga Karshe, DSS Ta Gurfanar da Godwin Emefiele a Gaban Babbar Kotun Tarayya

Daga Karshe, DSS Ta Gurfanar da Godwin Emefiele a Gaban Babbar Kotun Tarayya

  • Daga karshe, hukumar yan sandan farin kaya (DSS) ta gurfanar da dakataccen gwamnan CBN a gaban Kotu
  • Rahoto ya nuna jami'an DSS sun isa harabar babbar kotun tarayya mai zama Ikoyi, jihar Legas da misalin ƙarfe 9:18 na safiyar Talata
  • Tun a watan Yuni, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Emefiele daga matsayin gwamnan CBN

Lagos State - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kawo Mista Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), gaban kotu.

Jami’an DSS sun isa babbar kotun tarayya da ke zama a Ikoyi, jihar Legas, da misalin karfe 9:18 na safiyar ranar Talata 25 ga watan Yuli, 2023.

Godwin Emefiele yayin da ya isa Kotu.
Daga Karshe, DSS Ta Gurfanar da Godwin Emefiele a Gaban Babbar Kotun Tarayya Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta rahoto cewa an shirya gurfanar da Emefiele a gaban alkalin kotun mai shari'a Nicholas Oweibo kan zargin mallakar bindigogi ba kan ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Shiga Jimami Yayin Da Tsohon Shahararren Dan Wasan Ƙwallon Ingila Ya Rasu Yana Da Shekaru 69

Idan zaku iya tuna wa, a ranar 9 ga watan Yuni, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Mista Emefiele daga matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya kuma umarci Emefiele ya gaggauta miƙa harkokin jagoranci ga mataimakin gwamnam CBN mai kula da ɓangaren ayyuka, Folashodun Adebisi Shonubi.

Washe garin ranar da aka dakatar da shi, hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta sanar da cewa dakataccen gwamnan CBN, Emefiele na tsare a hannunta, "Bisa wasu dalilan bincike."

Emefiele ya maka DSS da AGF a Kotu

Sai dai bayan shafe kwanaki a tsare, Emefiele ta hannun lauyansa, Joseph Daudu, ya kai ƙarar DSS da Antoni Janar na ƙasa (AGF) inda ya roƙi alkali ya tabbatar masa da yancinsa na yawo kamar kowa.

A ranar 13 ga watan Yuli, 2023, babbar Kotun Abuja ta umarci DSS ta hanzarta gurfanar da tsohon gwamnan CBN ɗin a gaban Kotu idan ana zarginsa da aikata ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Har da kudi N300k: Lauya ya tono abubuwan da aka bankado a gidan Godwin Emefiele

Alƙalin Kotun ya yanke cewa ya zama dole a ba da belin Emefiele idan har ba a gurfanar da shi gaban Kotu ba cikin mako guda, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shugaba Tinubu Ya Cire Sunayen Wike da Ganduje Daga Cikin Ministoci? Gaskiya Ta Fito

A wani rahoton kuma Jigon APC ya fayyace gaskiya kan raɗe-raɗin cewa Tinubu ya cire sunan Ganduje da Wike daga jerin ministocin da zai naɗa.

Babban jigon APC ya yi kira ga magoya bayan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da na Nyesom Wike su kwantar da hankulansu kan batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262