PDP Ta Zargi APC Yayin Da Atiku Ya Tsallake Rijiya Da Baya a Gidansa
- Jam'iyyar PDP ta zargi APC da kokarin rufe bakin Atiku Abubakar kan shari'ar da ke gudana a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa
- An tattaro cewa wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sun farmaki Atiku a gidansa da ke Adamawa a yammacin ranar Lahadi
- Sai dai PDP, a wata sanarwa da ta saki a ranar Litinin, ta yi zargin cewa harin na iya samun nasaba da barazanar da APC ta yi a baya-bayan nan na rufe bakin Atiku
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da alhakin kitsa harin da aka kaiwa dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar.
A ranar Lahadi, 23 ga watan Yuli, wasu da ake zaton yan Boko Haram ne suka farmaki tsohon mataimakin shugaban kasar a gidansa da ke garin Yola, babban birnin jihar Adamawa kuma mahaifarsa.
Ganduje vs Al-Makura: Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Ya Kamata APC Ta Nada a Matsayin Shugabanta Na Kasa
PDP ta zargi APC da kokarin rufe bakin Atiku
Sai dai kuma, PDP a wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, ta yi zargin cewa, da ikirarin da wasu mahara suka yi, an dauki nauyin harin ne don raba Atiku da rayuwarsa kan dage da ya yi na kwato zabensa a kotun zaben shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa daga sakataren labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba, wanda aka wallafa a shafin jam'iyyar na Twitter, jam'iyyar adawa ta nuna zargin cewa harin yana iya samun nasaba da barazanar baya-bayanan nan da jam'iyyar APC mai mulki ta yi.
PDP ta sake caccar APC
Wani bangare na sanarwar ya ce:
"Jam'iyyar PDP ta tambaya, shin wannan harin da aka dakile a kan Atiku Abubakar kuma a wuri mai muhimmanci a Yola, Adamawa yana da alaka da barazanar ta da zaune tsaye na baya-bayan nan da APC ta yi da kuma haddasa rashin lafiya a kasar?"
Yan sanda sun kwamushe yan Boko Haram da suka yi kokarin kai hari gidan Atiku
A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu da ke zargin na da hannu a shirin kai hari gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar sun shiga hannu.
Wadanda ake kaman su hudu ana zarginsu da shirya kai hari a gidan dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar PDP a ranar Lahadi 23 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng